Sabbin ministoci: APC a Jihar Taraba ta yabawa Buhari gameda zabinsa

Sabbin ministoci: APC a Jihar Taraba ta yabawa Buhari gameda zabinsa

-Shugaban APC na jihar Taraba ya yabawa Buhari bisa zaben Mamman Sale a matsayin minista daga Taraba

-Ibrahim El-Sudi ya ce Mamman Sale ya cancanci wannan muqamin kasancewarsa masoyin Buhari tun shekaru aru-aru

-Shugaban yayi kira ga sauran masu neman mukamin da su rungumi kaddara kuma su cigaba da kare muradan jam'iyyar tasu

Alhaji Ibrahim El-sudi, shugaban APC na jihar Taraba ya jinjinama Shugaba Muhammadu Buhari bisa zabar Mamman Sale a matsayin minista daga jiharsa.

El-Sudi yayi wannan jawabin ne ranar Laraba a Jalingo a wata hira da yayi da manema labarai. Shugaban jam’iyyar ya bayyana mana cewa, gaba daya jagorancin jam’iyyar APC ta jihar Taraba na murna da zaben Sale kasancewarsa jigo a cikin jam’iyyar.

KU KARANTA:Da zafi-zafinsa: Anyi awon gaba da wasu mutum 3 kan babbar hanyar Legas-Ibadan

El-Sudi ya cigaba da cewa: “ Sanya sunan Sale a matsayin daya daga cikin ministoci zai karama APC kaimi a jihar Taraba wurin yin ayyukan cigaba domin sake hawa wani mataki kwatankwacin wannan.”

Haka zalika, yayi kira ga sauran ‘yan jihar wadanda ke kwadayin kujerar ministan da su rungumi kaddara su kuma zo a gudu tare domin a tsira tare gaba daya.

A cewar El-Sudi: “Sale ya kasance yana tare da Buhari tun a lokacin da ya fara neman takarar shugabancin kasa a karo na farko, sai ga shi a yau Allah ya masa gidan dogo an bashi muqamin minista.

“ A bayyane take Sale masoyin Buhari ne kuma dan jam’iyyar APC ne na hakika, a don haka muna taya shi murnar wannan mukamin da ya samu kuma muna masa fatan Allah ya mashi jagora.”

Kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ya bamu labarin cewa, gabanin a nada Sale a matsayin ministan Najeriya, ya kasance dan kasuwane sannan kuma mamba na hukumar gudanarwar Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Wukari wato Federal University Wukari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel