An damke matashin da ya hallaka mahaifinsa a Jigawa

An damke matashin da ya hallaka mahaifinsa a Jigawa

Jami'an yan sandan jihar Jigawa sun damke wani matashi dan shekara 25, Jamilu Harisu, da laifin kashe mahaifinsa mai shekaru 70.

Matashin, wanda ake zargi ya aikata aika-aikan ne saboda ya debi kwayoyi kafin ya kai wa mahaifinsa hari a gona.

Harisu ya kashe mahaifinsa ne a kauyen Makku dake karamar hukumar Garki na jihar Jigawa, inda ya buga masa fatanya a kai.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Audu Jinjiri, ya tabbatar da cewa mahaifin ya kwanta dama a asibitin Garki.

Yace: "Tuni yan sanda sun damkeshi da laifin kisan kai. An aika takardar tuhumarsa sashen binciken hukumar domin gudanar da bincike kafin gurfanar da shi."

A bangare guda, Kwana biyu kenan ana zub da jini a birnin tarayya Abuja yayinda yan kungiyar IMN wadanda akafi sani da yan Shi'a suka sake gwabzawa da jami'an yan sandan Najeriya a zanga-zangar da suka gudanar a shahrarriyar kasuwar Banex dake Wuse Abuja.

Bisa ga rahoton da yan sandan suka samu cewa yan Shi'an zasu fito yau misalin karfe 2 na rana, sai suka tare hanyar domin hanasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel