Rikicin yan Shia da Yansanda ya rutsa da wani dan bautan kasa, ya mutu har lahira

Rikicin yan Shia da Yansanda ya rutsa da wani dan bautan kasa, ya mutu har lahira

Sakamakon arangama da aka yi tsakanin jami’an rundunar Yansandan Najeriya dana kungiyar yan Shia a babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 22 ga watan Yuli, wani matashi dan bautan kasa, NYSC, ya gamu da ajalinsa.

Legit.ng ta ruwaito wannan matashi dan bautan kasa mai suna Precious Owolabi yana aiki ne da gidan talabijin na Channels a matsayinsa na dan jarida mai neman sanin makaman aiki, a lokacin da rikicin ya rutsa dashi yayin da ya tafi daukn rahoto.

KU KARANTA: Fadan yan Shia da Yansanda: Buhari ya shiga ganawar sirri da hafsoshin tsaro

Rikicin yan Shia da Yansanda ya rutsa da wani dan bautan kasa, ya mutu har lahira
Rikicin yan Shia da Yansanda ya rutsa da wani dan bautan kasa, ya mutu har lahira
Asali: Facebook

Gidan talabijin na Channels ta tabbatar da mutuwar Owolabi a labaranta na karfe 10 na daren, inda tace a ranar Litinin ne yan Shia da Yansanda duka yi arangama a daidai sakatariyar ma’aikata dake Abuja, a yayin hargitsin ne aka harbi Owolabi, wanda ya mutu yayin da aka garzaya dashi Asibiti.

Baya ga Precious, yan Shia sun kashe wani babban jami’in Dansanda mai rike da mukamin mataimakin kwamishinan Yansandan babban birnin tarayya Abuja, Usman Umar Belell, dan asalin jahar Adamawa.

Haka zalika Yan shia sun kona wani karamin ofishin hukumar bada agajin gaggawa, NEMA, tare da motocin aikin hukumar guda biyu, duk a yayin wannan hargitsi na ranar Litinin, sai dai kungiyar Shia ta musanta hannu cikin kashe Dansandan da kona ofishin NEMA.

Kaakakinta, Abdullahi Musa ne ya bayyana haka, inda yace Yansanda ne suka kashe mataimakin kwamishina Usman yayin da suka kaddamar da harbin mai kan uwa da wabi, a haka suka kashe yan shia 17.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel