Dubun dan fashi da ke buya a cikin kabari ta cika

Dubun dan fashi da ke buya a cikin kabari ta cika

Jami'an Ofishin rundunar 'yan sandan kasar Ghana da ke Kaneshi sun kama wani matashi mai shekaru 25 da ake zargin cewa ya na daga cikin gungun barayin da ke kai wa fasinjoji farmaki da daddare a kan gadar makabartar Awudome.

A cewar 'yan sanda, matashin, Isaac Appiah, kan ruga cikin duhuwar makabartar tare da buya a daya daga cikin kabarurrukan da babu gawa a cikinsu duknlokacin da ya yi fashi aka biyo shi.

Dubun shi ta cika ne bayan jami'an 'yan sanda da ke sintiri sun bi shi bayan ya yi wani fashi kuma ya ruga cikin duhuwar makarbartar.

Yanzu haka matashin na hannun jami'an 'yan sanda na ofishin Kaneshi inda ya ke bayar da hadin kai a binciken da suke gudanar wa.

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta mika tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram 151 ga gwamnatin jihar Borno

Kwamandan 'yan sandan ofishin Kaneshie, SP Ernest Acheampong, ya ce an kama Appiah ne da misalin karfe 10:00 na daren ranar Laraba bayan ya yi wata mata fashi.

Dubun dan fashi da ke buya a cikin kabari ta cika
Dubun dan fashi da ke buya a cikin kabari ta cika
Asali: Twitter

SP Acheampong ya ce Appiah ya yi farat ya fito daga cikin makarbatar, wacce ba a amfani da ita, inda ya kwace jakar hannu ta matar, kuma nan da nan ya kara bacewa zuwa cikin duhuwar makabartar.

Ya kara da cewa mai laifin ya dade ya na aikata wannan hali kullum da daddare sannan ya bace zuwa cikin duhuwar makabarta inda ya ke buya a cikin kabari kafin daga bisani, bayan sahu ya dauke, ya fito ya shiga Otal ya kwana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel