Karshen duniya: Ma'aikacin gidan 'Zoo' ya yi wa macen goggon biri ciki

Karshen duniya: Ma'aikacin gidan 'Zoo' ya yi wa macen goggon biri ciki

A wani yanayi mai daure kai da matukar ban mamaki, an gano wani mutum, mai shekaru 38 da ke aiki a wani gidan 'Zoo' da ke Kalimanta a yankin tsibirin Borneo na kasar Malaysia, da ke lalata da dabbobin da yake kula da su.

Hukumar gidan 'Zoo' din da mutumin ke aiki ta gano abinda yake yi ne ta hanyar amfani da boyayyun na'urorin nadan faifan bidiyo bayan an fara zarginsa da aikata halayyar da ba ta dace ba ga dabbobin da ya ke kula da su. An yi amfani da boyayyun na'aurorin wajen kama shi yayin da yake aikata mummunan dabi'ar.

Ma'aikatan gidan 'Zoo' din da ke cike da mamaki, sun bayyana cewa ya dauke su lokaci mai tsawo kafin su gano abinda ke faruwa.

"Sha'awar wasu dabbobi na motsawa ne lokacin da za a basu abinci," a cewar Akhiroel Yahya, ma'aikacin gidan 'Zoo' mai gogewar aiki ta fiye da shekaru 14.

"Zargin mu ya kara karfi ne bayan mun gano cewa Marylin, macen goggon biri mafi yawan shekaru da muke da ita, na da juna biyu. Tsawon shekaru 10 kena da muka ware mata wurin ajiya saboda masifar ta, a saboda haka bamu ga yadda za ai ta samu juna biyu ba," a cewar Yahya.

"Da farko ba mu fahimci mene ne ke faruwa ba," a cewar darektan gidan 'Zoo' din, Abdoel Hakim.

DUBA WANNAN: Barayi sun yi wa 'yar sanda duka, sun yi mata tsirara a kasuwar Abuja (Bidiyo)

Sannan ya kara da cewa, "sai bayan da muka yi amfani da na'urorin nadan bidiyo na sirri sannan muka gano gaskiyar da ta girgiza mu, kuma ta bamu tsoro."

Sai dai, da aka tunkari ma'aikacin da ya aikata hakan, ya musanta cewa ya aikata laifin da ake tuhumarsa da shi. Amma daga baya ya shaida wa jami'an 'yan sanda cewa duk abinda ya aikata da aminncewar Marylin, macen goggon birin.

"Ya ce duk abinda ya aikata, da amincewar dabbobin," a cewar wani jami'in dan sanda, Abubakar Jaar.

"Ya ce shi da dabbobin suna kaunar juna, kuma ya bayar da hakuri a kan cikin da ya yi wa macen goggon birin," kamar yadda ya shaidawa kafafen yada labarai na cikin gida.

Sannan ya kara da cewa bai san cewa mutum zai iya yiwa jinsin biri ciki ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel