Yanzu-yanzu: Yan Shi'a sun saba umurnin gwamnati, sun cigaba da zanga-zanga a Abuja
Mabiya Sheik Ibrahim El-Zakzaky wadanda aka fi sani da Shi'a sun cigaba da gudanar da zanga-zanga duk da umurnin hukumar yan sanda da ta hana taro a birnin tarayya illa farfajiyar Unity Fountain.
Yan Shi'an sun bazama da safiyar Juma'a suna gudanar da zanga-zanga a babbar hanyar Aguiyi Irinsi dake birnin taayyar inda suke kira da shugaba Muhammadu Buhari ya sakeshi.
Suna zanga-zangar ne kan rashin jin dadinsu da shari'ar kotu na jiya inda ta hana shugaban nasu, El-Zakzaky, dama fita waje jinya.
Babban kotun dake jihar Kaduna ta dakatad da sauraron karar shugaban kungiyar akidar Shi'a inda yake bukatar fita kasar Indiya jinya, zuwa ranar 29 ga watan Yuli, 2019.
Gabanin zama kotun yau, hankalin mazauna birnin Kaduna ya tashi yayinda jami'an tsaro suka rufe dukkanin hanyoyin kotu.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya taya Malam Abubakar murna a bisa karramawar da ya samu a kasar Amurika
Sheik Ibrahim Zakzaky na gurfana a kotu ne kan laifuka da dama wanda ya hada da tunzura mabiyansa suna fito-na-fito da hukuma.
A ranar 12 ga watan Disamba, 2015, hukumar Sojin Najeriya sun kai mumunan hari hedkwatan yan Shi'a, Hussainiyah, dake unguwar Gyallesu, karamar hukumar Zariya dake jihar Kaduna, inda sukayi batakashi da yan Shi'a kuma sukayi gaba da shugabansu.
Kusan shekaru hudu kenan, yana tsare a hannun hukumar DSS bayan likitoci sun tabbatar da cewa ya rasa idonsa daya kuma sashen jikinshi ya shanye.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng