Harkar tsaro za ta inganta a Najeriya - Jonathan

Harkar tsaro za ta inganta a Najeriya - Jonathan

A ranar Alhamis, tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan, ya kyautata zato na bayar da tabbaci ga al'ummar kasa kan cewa harkokin tsaro za su inganta nan ba da jimawa ba.

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, a ranar Alhamis, 18 ga watan Yuli, ya ce al'ummar Najeriya su sha kurumin su tare da bayar da tabbacin samun aminci da kwanciyar hankali a yayin da tsaro zai inganta nan ba da jimawa ba.

Wannan tabbaci na tsohon shugaban kasa na zuwa ne a yayin da ya halarci bikin gabatar da wani littafi mai taken Not by Might Nor by Power wato babu iyawa babu iko da kuma kaddamar da gidauniyar Nicholas Okoha a garin Abuja.

A cewar sa, rashin tsaro ya kasance tare da yaduwa a kasar nan tsawon wani lokaci da a halin yanzu ya kamata a yi taron dangi gami da yin rubdugu wajen magance wannan mummunan kalubale.

Jonathan ya ce nan ba da jimawa duk wani kalubale da kasar nan take fuskanta zai zama tarihi a sakamakon yadda shugabanni da suka hadar da 'yan siyasa da kuma sarakunan gargajiya suka daura damarar ta tsayuwar daka.

KARANTA KUMA: Tsohon gwamnan jihar Oyo ya yi watsi da tayin kujerar minista a gwamnatin Buhari

Tsohon shugaban kasar ya kuma nemi dukkanin jagorori da masu rike da madafan iko a kowane mataki cikin kasar nan da su bayar da gudunmuwar fidda Najeriya zuwa tudun tsira tare da jin kan na kasa da su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel