Najeriya za ta fara sayarwa India 10% na danyen man fetur din ta - NNPC

Najeriya za ta fara sayarwa India 10% na danyen man fetur din ta - NNPC

Kamfanin Tace Man Fetur ta Kasa (NNPC) ta ce za ta fara sayarwa kasar India kashi 10 cikin 100 na danyen man fetur din ta domin taimakawa kasar warware matsalar makamashi da ta ke fama da shi.

Kasar India wacce ita ce kasa mafi yawan al'umma na biyu a duniya tana bukatar man fetur daga wasu kasashe domin warware matsalar makamashi da kasar ke fama da shi a halin yanzu.

Shugaban NNPC, Mele Kyari ya ce Najeriya za ta cigaba da tallafawa India wurin warware matsalar makamashin da ta ke fama da shi ta kowanne hanya da za ta iya.

DUBA WANNAN: Buhari ya canja hotonsa da ake amfani da shi a hukumance

Mai magana da yawun hukumar, Ndu Ughamadu ya ce Mista Kyari ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis yayin da wakilin kasar Indiya, Abhay Thakur ya kai ziyara hedkwatan hukumar da ke Abuja.

A cewar Mr Ughamadu, shugaban na NNPC ya ce yarjejeniyar fahimatar juna da Najeriya da India suka rattaba hannu a kai zai karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Mr Kyari ya ce NNPC a shirye ta ke wurin hadin gwiwa da India domin ganin kasashen biyu sun amfana da juna.

"A shirye mu ke mu zauna tare da tawagar 'yan kasuwa na Indiya domin kasahen biyu su amfana. Ba za a bar kowanne dama ta kasuwanci ta wuce ba," a cewar Kyari.

A bangarensa, Wakilin kasar Indiya ya mika godiyarsa ga mahukuntan NNPC kan sabunta kwangilar samar da man fetur da aka bawa kamfanonin kasar uku damar shiga.

Mr Abhay ya bukaci Najeriya ta kara adadin danyen man fetur din da za ta rika sayarwa India domin samun damar warware matsalar da suka fama da ita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel