Yan iska sun far ma ayarin wani basaraken Yarbawa kan rigimar fili

Yan iska sun far ma ayarin wani basaraken Yarbawa kan rigimar fili

Sarkin Araromi-Obu a jihar Ondo, Oba Aderemi Adelola, ya tsallake rijiya da baya a lokacin da wasu yan iska suka far ma ayarinsa da hari.

An rahoto cewa Oba Adelola ana a hanyarsa ta dawowa daga wani tafiyar aiki a Akure, babbar birnin jihar Ondo, lokacin da aka kai masa harin.

An tattaro cewa wasu yan iska da ke ikirarin mallakar wani fili a garin ne suka kai wa motarsa da na ayarinsa hari.

Da yake jawabi ga manema labarai a madadi kungiyar ci gaban Araromi-Obu, Sanata Omololuwo Meroyi, a Akure yace: “An kashe mutane biyu, mutane takwas sun jikkata yayinda aka kona gidaje biyar a Ago-Alaye, wani gari da ke yankin Odigbo.”

Meroyi yace: “Mutanen Araromi Obu sun fuskani mumunan hari daga makwabtansu na Ikale kan hukuncin da wata babbar kotun Akure ta yanke, wanda ya bai wa mutanen Ikale wani yanki na kasarsu.”

A halin da ake ciki, kakakin yan sandan jihar, Mista Femi Joseph, yace an daidaita lamarin.

Yace an tura jami’an yan sandan tafi da gidanka, sannan kuma jami’an yan sandan sa kai daga yankin Okitipupa sun sasanta lamarin.

KU KARANTA KUMA: Kasar Amurka za ta karrama Limamin da ya boye Kiristoci sama da 200 a Masallaci a lokacin rikicin Jos

A cewar Joseph, “Ina sane da cewar suna fada, amma an tura jami’anmu domin su dawo da zaman lafiya a yankin.

“Jami’anmu sun kama wasu mutanen da ke da nasaba da rikicin.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel