An damke yan luwadi biyu a birnin tarayya, Abuja
Hukumar yan sanda a ranar Alhamis ta gurfanar da wasu matasa biyu a kotun Grade 1 dake unguwar Kabusa Abuja kan tuhumar aikata luwadi.
Matasan biyu masu suna, John Samuel da Mohammed Sani mazauna unguwar Dakwa ne a cikin birnin tarayya Abuja.
Lauyan gwamnati, John Ijagbemi, ya bayyanawa kotu cewa wadannan matasa sun aikata aikin alfashan ne ranar 18 ga watan Yuni, 2019.
John Ijagbemi ya bayyana cewa a ranar 18 ga Yuni misalin karfe 1:30 na dare, jami'an yan sandan Garki, birnin tarayya masu sintiri sun damke matasan suna luwadi da juna a unguwar Garki.
Ya laburtawa kotu cewa yayin bincike, an gano cewa matasan sun kasance suna aikata luwadi tun shekarar 2018.
KU KARANTA: Bayan makonni takwas, gwamnoni 26 basu nada kwamishanoni na
Alkalin kotun, Aliyu Kagarko, ya basu beli milyan biyu-biyu da wanda zai tsaya musu. An dakatad da karan zuwa ranar 25 ga Yuli, 2019.
Mun kawo muku rahoton cewa Fitacciyar mawakiyar 'Pop' din nan Janet Jackson kanwa a gurin shaharren marigayin mawakin nan Micheal Jackson, ta na daya daga cikin shahararrun mawakan da zasu yi waka a kasar Saudiyya.
Bayan ita kuma akwai shahararren mawakin nan na 'Rap' 50 Cent wanda shima zai je kasar ya baza tashi iyawar. Rahotanni sun nuna a satin da Nicki Minaj ta nuna cewar baza tayi wasan a kasar ba, sai aka gayyato wadannan mawakan guda biyu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng