Karshen zancen kenan: Kotu ta bada belin Hanan, matar da ta cakawa mijinta wuka a kahon zuci

Karshen zancen kenan: Kotu ta bada belin Hanan, matar da ta cakawa mijinta wuka a kahon zuci

- Wata kotu a jihar Kano ta saki Hanan, matar da tayi kokarin kashe mijinta ta hanyar caka masa wuka a kirji

- Kotun ta bayar da belin Hanan ne bayan musayar yawu tsakanin lauyan gwamnati da kuma lauyan da yake kare ta, inda a take a wajen kotu ta bayar da belinta

- Hanan ita ce wacce mijinta ya bayyana cewa bata da aiki sai fita tana tarayya da wasu mazajen a titi

Wata babbar kotu mai lamba daya a jihar Kano ta tabbatar da ba da belin Fatima Hamza wacce aka fi sani da Hanan.

Ana zargin Hanan da kokarin kashe mijinta mai suna Sa'eed Hussain bayan ta caka masa wuka a kahon zuci.

Shugabar kungiyar lauyoyi mata ta Najeriya (FIDA) Barrister Huwaila Mohammed ta bayyanawa kotu cewa tuhumar da hukumar 'yan sanda ke yiwa Hanan ba ta da tushe bare makama, saboda fada ne ya hadata da mijin nata ya doketa har hakorinta ya fita, ita kuma da taji zafi ta dauki wuka ta soka masa, hakan yasa suka yi kare jini biri jini.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Haka kawai an wayi gari miliyan 200 tayi batan dabo a shagon Sahad Store na Kano

Barrister Lamido Abba Soron Dinki, wanda yake zaune a matsayin lauyan gwamnati bai kalubalanci maganar Barrister Huwaila ba, hakan ne ya sanya kotun ta bayar da belin Hanan a take a wajen.

Hanan ita ce dai matar da ake zargin ta cakawa mijin ta wuka a kahon zuci, hakan yayi sanadiyyar kwantar dashi a asibiti na tsawon wasu kwanaki.

Da aka tambayi Hanan dalilin caka masa wukar ta bayyana cewa tunda suka yi aure bashi da aiki sai dukanta, amma kuma bayan mijin ya farfado maganar ta canja yayin da ya bayyana cewa matar tasa tana tarayya da wasu samarin ne a titi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel