Zakzaky ya nemi kotu ta bashi daman tafiya kasar India don duba lafiyarsa

Zakzaky ya nemi kotu ta bashi daman tafiya kasar India don duba lafiyarsa

Shugaban kungiyar yan shia na Najeriya, Ibrahim Zakzaky tare da matarsa Zinatu sun nemi wata babbar kotun jahar Kaduna ta basu izinin fita kasar India domin su duba lafiyarsu da suka ce tana tabarbarewa.

Gwamnatin jahar Kaduna tana tuhumar Zakzaky ne a gaban babbar kotun a kan laifukan da suka shafi kisan kai, taro ba bisa ka’ida ba, tayar da hankulan jama’a da kuma sauran laifuka da dama.

KU KARANTA: Akasi: kuskuren rubutu ya zaunar da wani mutumi a Kurkuku tsawon shekaru 14

Sai dai rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito daraktan shigar da kara na gwamnatin jahar Kaduna, Dari Bayero yace a ranar Alhamis ne Alkali D.H Khobo zai cigaba da sauraron karar.

Mista Bayero ya bayyana ma majiyar Legit.ng cewa Zakzaky ya mika bukatarsa ga kotun ne a ranar Laraba, inda ya nemi ta bashi daman zuwa Asibitin Metanta dake birnin New Delhi a kasar Indiya domin a duba lafiyarsa, kuma ya yi alkawarin zai dawo Najeriya don cigaba da shari’ar da zarar an sallameshi.

Wannan shine Alkali na biyu dake sauraron karar da gwamnatin jahar Kaduna ta shigar da Zakzaky, inda a baya mai sharia Gideon Kurada ne yake sauraron karar, amma a ranar 25 ga watan Afrilu ya dage sauraron karar har sai baba ta ji.

Alkalin ya dage karar ne domin ya gudanar da aiki a matsayin Alkalan da aka zaba a kwamitin sauraron korafe korafen zaben shugaban kasa dana yan majalisun dokokin Najeriya dake zamanta a jahar Yobe.

Shima babban lauyan Zakzaky, Femi Falana ya sha nanata bukatar sakin wanda yake karewa dsa matarsa Zinat, inda yace suna bukatar kyakkyawar kula ga lafiyarsu, saboda rabonsu da samun kulawa tun watan Disambar shekarar 2015.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel