Gwamnatin Kaduna za ta rufe makarantun kudi wadanda ba su yin abinda ya dace, inji Kwamishina

Gwamnatin Kaduna za ta rufe makarantun kudi wadanda ba su yin abinda ya dace, inji Kwamishina

-Gwamnatin Kaduna ta shirya tsaf domin magance matsalar bayar da ilimi maras inganci a fadin jihar

-Kwamishinan ilimin jihar Kaduna ne ya bada sanarwar cewa gwamnati na da niyyar rufe duk makarantar kudin da ta gagara ba yara ilimi mai nagarta

-Dr Makarfi ya ce barin irin wadannan makarantun zai haifar da tabarbarewar cigaban ilimin jihar Kaduna a daidai lokacin da ake son a ga abubuwa sun gyaru

Gwamnatin Kaduna ta ce za ta bibiyi sahun makarantun kudin dake jihar domin rufe wadanda ba su yin abinda ya dace, a matsayin yinkurin da take na tabbatar da a na bai wa yaran jihar ilimi mai inganci.

Kwamishinan ilimin jihar, Dr Shehu Makarfi ne ya bada wannan sanarwar ranar Laraba a Kaduna, lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN.

KU KARANTA:Ku bar aibata kabilar Fulani – Matthew Kukah

Makarfi ya bayyana shirin na gwamnatin Kaduna inda ya ce, za’a nemo haqiqanin mazaunin dukkanin makarantun kudin jihar. A cewarsa hakan zai sauwake wa ma’aikatar ilimi aiki, ta yadda za ta iya sanya ido kan makarantun ko su na koyarwa yadda doka ta tsara.

Kwamishinan ya ce: “ Kwanan nan zamu fara bin sahunsu, wadanda muka samu su na yin abinda ya dace wurin koyarwa zamu ba su kwarin gwiwar cigaba. Idan kuma muka tarar da akasin hakan zamu rufe makarantar ne.

“ Wasu daga cikin wadannan makarantun kudi kawai suke nema, ba ruwansu da nagartar ilimin da suke bayar wa. Har ila yau, akwai wadanda ke kokari amma dai ba su cinma mafi karancin matsayin da ya kamata a ce makaranta ta cimma ba, wadannan zamu iya ba su lokaci domin su sake gyara tsarinsu.

“ Abinda kawai ba zamu lamunta ba shi ne, barin makarantun da ba samar da ilimi mai inganci ke gabansu ba. Idan muka bar ire-iren wadannan makarantu to tabbas makomar ilimin yaranmu na cikin halin o ni ‘ya su.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel