Buhari ya aika sakon ta'aziyya ga gwamna Ahmed Makarfi

Buhari ya aika sakon ta'aziyya ga gwamna Ahmed Makarfi

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa ha tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon shugaba jam'iyyar PDP, Ahmed Mohammed Makarfi, bisa ga rashin mahaifinsa, Alhaji Muhammadu Na'iya, Majidadin Zazzau.

Hakazalika Buhari ya mika saon jaje ga gwamnati, al'ummar jihar Kaduna, da masarautar Zazzau kan rashin Majidadin Zazzau, wanda kasance babban murya a cikin al'ummarsa.

Buhari ya aika wannan sakon ta mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ne da yammacin Talata. Ya yi addu'an Allah ya jika mamacin, ya rahshesa kuma ya karawa iyalinsa hakuri.

Mun kawo muku rahoton cewa Allah ya yiwa mahaifin tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Alhaji Ahmed Mohammed Makarfi, rasuwa.

An sanar da rasuwarsa ne da ranan nan bayan Sallar Azahar.

Sanarwar yace: "Mahaifin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi ya rasu. Za;a gudanar da jana'izarsa misalin karfe 4 na yamma bisa ga koyarwan addinin Musulunci. Allah ya jikanshi da rahama."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel