Ta shiga hannu: An damke matar da ta antayawa mijinta ruwan zafi don zai kara aure

Ta shiga hannu: An damke matar da ta antayawa mijinta ruwan zafi don zai kara aure

Hukumar yan sanda a jihar Kano ta tabbatar da damke matar aure mai suna, Aisha Ali, wacce ya antayawa maigidanta ruwan zafi a azzakari. kamfanin dillancin labarai NAN ya bada rahoto.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna, ya alanta damketa a wani jawabi da yayi a Kano ranar Talara inda yace wannan abu ya faru ne a kauyen Feyen-feyen da ke karamar hukumar Danbatta.

Haruna ya ce hukumar ta samu labarin abinda ya faru ne ranar Lahadi daga bakin maigarin Feyen-feyen cewa Aisha ta zubawa maigidanta ruwan zafi a cinya da azzakari a ranar Juma'a.

Yace: "Mijin ya samu rauni a azzakarinsa. A yanzu haka yana jinya a babbar asibitin Danbatta kuma yana samun lafiya."

Yace bayan wannan mumunan abu da Aisha ta aikata, sai ta gudu jihar Jigawa.

KU KARANTA: Marasa kishin kasa ne masu kushe tsaron Najeriya, Buhari ya mayarwa Obasanjo martani a fakaice

DSP Haruna ya ce samun labarin haka ke da wuya, sai hukumar yan sanda ta tura jami'an rundunar atisayen Operation Puff Adder inda suka lalubota a inda take boue a Babura, jihar Jigawa.

Binciken farko-farko da aka gudanar ya nuna cewa ta aikata wannan abu ne kawai don mijin na kokarin kara aure.

Ya ce kwamishanan yan sandan jihar ya bada umurnin mayar da al'amarin sashen gudanar da binciken hukumar domin gudanar da bincike mai zurfi.

Haruna ya kare da cewa ana kammala bincike za'a gurfanar da ita a kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel