Kar ku bari El-Zakzaky ya mutu a gidan kaso, Falana ya gargadi gwamnati tarayya

Kar ku bari El-Zakzaky ya mutu a gidan kaso, Falana ya gargadi gwamnati tarayya

- Femi Falana ya gargadi gwamnatin tarayya game da lamarin shugaban kungiyar 'yan shi'a Ibrahim El-Zakzaky

-Falana a cikin jawabinsa ya ce idan har gwamnati ta bari El-Zakzaky ya mutu a gidan yari ba mamaki abinda ya faru a shekarar 2009 zai maimaitu a wannan lokaci

-Kamar yadda rahotanni ke nunawa El-Zakzaky na fama da rashin lafiyar da ke buqatar kulawa ta musammman

Babban lauyan nan wanda ke fafutukar kare haqqin bil adama, Femi Falana (SAN) ya furta kalaman gargadi ga gwamnatin Najeriya kan cigaba da tsare Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da take yi.

Lauyan yayi gargadin nasa ne ta hanyar wani saqo da ya aikawa tashar labarai ta Channels TV a ranar Talata. Falana a cikin zancen nashi ya bayyana mamakinsa bisa hawa kujerar naqi da gwamnati tayi game da jagoran shi’an duk da cewa kotu ta bada umarni sakinsa.

KU KARANTA:Mun ci karfin matsalar tsaron Najeriya, masu ce-ce kuce nayi ne kawai saboda siyasa – Buratai

Bugu da kari, ya sake magana kan rashin lafiyan jagoran na kungiyar shi’a inda yake cewa abu mafi dacewa da El-Zakzaky shi ne a fita da shi kasar waje domin nemo masa magani.

Har ila yau, babban lauyan ya janyo hankalin gwamnatin Najeriya bisa abinda kan iya biyo baya idan har shugaban shi’an ya mutu a hannun hukuma. A cewarsa za’a iya samun barazanar rashin tsaro wadda kafin a maganceta sai an wahala kwarai da gaske.

Kari a kan wannan, Falana ya lissafo wasu daga cikin zanga-zangar da aka gudanar kwanan nan a Abuja wadanda suka rikide zuwa fada har ma da kashe-kashen wasu mutanen.

Haka zalika, lauyan kare haqqin bil adaman ya kawo mana abinda ya faru a shekarar 2009 sakamakon kisan Muhammad Yusuf shugaban kungiyar Boko Haram na wancan lokacin, inda ya ce kisan nashi ne dalilin da ya sanya kungiyar ta soma fitinar al’umma.

A karshe ya sake nanata kalamansa na gargadin gwamnatin tarayya, da kada ta bari El-Zakzaky ya mutu a hannunta saboda a cewarsa, yanzu kasar nan ba ta shirya fuskantar matsalar rashin tsaro irin wannan ba kasancewar wadanda take fama da su sun isheta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel