Yanzu-yanzu: Marasa kishin kasa ne masu kushe tsaron Najeriya, Buhari ya mayarwa Obasanjo martani a fakaice

Yanzu-yanzu: Marasa kishin kasa ne masu kushe tsaron Najeriya, Buhari ya mayarwa Obasanjo martani a fakaice

-Shugaba Buhari yayi martani zuwa ga tsohon shugaban kasa a fakaice ba tare da ya ambaci sunansa ba

-Shugaban kasan ya fadi wannan maganar tasa ne a fadar gwamnatin tarayya ta Villa dake Abuja ranar Talata lokacin da yake karbara bakoncin kungiyar BCO

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya mayar da martani ga mutanen dake korafin cewa babu tsaro a Najeriya a yau inda ya kirasu da suna ‘marasa kishin kasa’.

Idan baku manta ba, a jiya Litinin ne tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya rubutawa Buhari wata budaddiyar wasika inda yake sukar lamarin tsaron a yau da ma wasu abubuwa da dama game da gwamnatin Shugaba Buhari.

KU KARANTA:Mun ci karfin matsalar tsaron Najeriya, masu ce-ce kuce nayi ne kawai saboda siyasa – Buratai

Shugaba Buhari yayi wannan martanin ne ranar Talata a fadar gwamatin tarayya ta villa, yayin da yake karbar bakoncin majalisar zartarwar kungiyar Buhari Campaign Organisation (BCO). Inda ya ce, marasa kishi ne kadai za su iya sukar lamarin tsaron kasar nan, ba tare da ya kira suna ba.

A cewar shugaban kasan, ko wace kasa a duniyar nan na da irin nata matsalolin tsaro. Ya kara da cewa akwai sabbin matsalolin ‘yan bindiga da kuma garkuwa da bil adama a kasashen duniya a yau.

Cikakken bayani na nan tafe………

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel