Shaidan PDP ya bayyana abinda mahaifinsa ya fada masa a kan asalin Atiku

Shaidan PDP ya bayyana abinda mahaifinsa ya fada masa a kan asalin Atiku

Daya daga cikin shaidun da Atiku Abubakar da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) suka gabatar a gaban kotun sauraron zaben shugaban kasa (PEPT) ya yi ikirarin cewa mahaifinsa ne ya fada masa cewa a Najeriya aka haifi Atiku shi yasa ya ce Atiku dan Najeriya ne.

Mai bayar da shaidan, Mohammed Hayatu da ya ce ya yi murabusa daga Hukumar Kwastam ya ce mahaifin na sa ya rasu.

Hayatu ya kuma ce ya san cewa wani bangare na jihar Adamawa sashi na na Arewacin Kamaru kafin daga bisani aka dawo da shi Najeriya bayan mutanen yankin sunyi zabe kuma suka nemi da dawo da su Najeriya a 1961.

DUBA WANNAN: Yadda muka hana a tsige Obasanjo - Yakubu Gowon

Shaidan ya ce Jadda inda aka haifi Atiku bai taba kasancewa karkashin Kamaru ba.

A baya, wani shaida ta aka gabatar mai suna Magdiel Samaki wanda ya ce shi wakilin Najeriya ne kasar Romania ya ce ba zai iya tuna wani lokaci da wata yanki na Arewacin Kamaru a 1961 tayi zabe na komawa Najeriya ba.

Ku biyo mu domin karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel