Allah ya kyauta: 'Yan daukar amarya sun kashe wani yaro a wajen neman abincin shi a jihar Kano

Allah ya kyauta: 'Yan daukar amarya sun kashe wani yaro a wajen neman abincin shi a jihar Kano

- Wasu 'yan kai Amarya a karamar hukumar Gaya dake jihar Kano sun banke wasu yara guda biyu a lokacin da suke zaune suna sana'ar gyaran fitila

- Lamarin ya biyo bayan irin tukin ganganci da direbobin daukar Amaryar suke a lokacin da suka ciko motocinsu da 'yan mata

- Lamarin yayi sanadiyyar mutuwar daya daga cikin yaran, inda daya kuma ya ji munanan raunika a jikinshi

Ranar Asabar 12 ga watan Yuli, 2019, wasu masu daukar Amarya da suke gudun ganganici a karamar hukumar Gaya dake jihar Kano suka doke wasu yara guda biyu.

Daya daga cikin yaran kanshi da kirjinsa sun fashe, inda ya mutu a take a wajen, yayin da dayan kuma ya samu munanan raunika a jikinsa.

Rahotanni sun nuna cewa marigayin yana sana'ar sa ta gyaran fitla ne a gefen titi shi da wasu yara abokanansa, inda matan aure suke aiko da fitilun su domin a gyara musu.

KU KARANTA: Allura zata tono garma: Hon. Abdulmumini Jibrin yayi barazanar tona yadda aka yi magudin zaben 2019 a jihar Kano

Lamarin ya faru ne yayin da 'yan daukar Amaryar suka ciko mota da mata suke gudu suna tukin ganganci akan titin da yaran suke neman na abinci.

Motocin na zuwa kusa yaran daya ta kwace daga hannun direban tayi kan yaran, a take taa banke guda biyu daga ciki. A take a wajen daya ya mutu dayan kuma da yaji raunika aka garzaya dashi asibiti domin duba lafiyarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel