Yanzu-yanzu: Obasanjo ya sake aikewa Buhari wasika, ya caccakeshi

Yanzu-yanzu: Obasanjo ya sake aikewa Buhari wasika, ya caccakeshi

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya sake aikewa shugaba Muhammadu Buhari wasika inda yake gargadin cewa Najeriya na cikin halin Ha'ula'i kuma shugaban kasa ne kadai ke iya ceto ta.

Ya ce tun lokacin da Buhari ya hau mulki, Najeriya ta shiga cikin mumunan halin rashin tsaro wanda ba'a taba gani ba a tarihin kasar nan.

A wasikar da ya aika ranar 15 ga Yulin 2019, Obasanjo ya ce duniya, musamman kasashen Turai, suna gargadin wani irin barkewa da ka iya faruwa a Najeriya wanda ba za'a iya tarewa ba.

Ya gargadi Buhari kan cewa muddin yana son ya kawo karshen rashin jituwa tsakanin kabilu, wajibi ne ya daina nuna kabilanci da bangaranci.

Hakazalika, Obasanjo ya yi kira ga makiyaya su fito su bayyana abubuwan da suke bukata domin a samu zaman lafiya sabanin kashe-kashen dake faruwa a fadin kasa.

Ya yi kira da hukumar sojin Najeriya ta daina cin mutuncin jami'an soji saboda hakan ya rage musu karfin gwiwa kuma hakan zai shafin tsaron kasar.

Obasanjo ya yi wannan magana domin caccakan babban hafsan sojin Najeriya, Laftanan Janar Tukur Buratai, wanda ya daura laifin koma bayan da ake samu wajen yaki da Boko Haram kan jami'an sojojin dake faggen fama.

Wasikar Obasanjo ya biyo bayan kisan diyar shugaban kungiyar Yarabawa, Afenifere, Reuben Fasoranti, da masu garkuwa da mutane sukayi a makon da ya gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel