Ambaliyar ruwa ta mamaye wasu makarantu a Jigawa

Ambaliyar ruwa ta mamaye wasu makarantu a Jigawa

-Wasu makarantu a karamar hukumar Hadejia dake Jihar Jigawa sun cika maqil da ruwa

-Sakataren ilimi na karamar hukumar Musa Garba ne ya tabbatar mana da aukuwar wannan lamari amma da ya ce an dauke matakin sama wa yaran wani wurin karatu

-Musa Garba ya miqa rahoton wannan al'amari ga Hukumar bayar da ilimi ta bai daya ta jihar Jigawa domin a kawo masu dauki

Ruwan sama mai nauyi da aka jera kwanaki a nayi a garin Hadejian jihar Jigawa ya yi sanadiyar mamaye makarantun firamare biyar da kuma wasu na sakandare dake garin na Hadejia, kamar yadda wani jami’i ya shaida mana ranar Juma’a.

Sakataren ilimi na karamar hukumar Hadejia, Alhaji Musa Garba ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN cewa makarantun da wannan ambaliyar ruwa ta shafa sun hada da; makarantar karamar sakandare ta Hamza Abdullahi Junior Secondary, Haruna Junior Secondary School, Makarantar Firamaren Matsaro, Makarantar Firamaren Usman Maidashi da kuma Makarantar Firamaren Haruna.

KU KARANTA:Duniya ina zaki damu: Wata mata ta kashe ubangidanta kan ya qi biyanta N525

Garba ya kara da cewa, an sauya ma daliban makarantun wani wuri na wucen gadi, inda za su rika yin karatu a wasu makarantu da ambaliyar bat a shafa ba har zuwa lokaci da ruwan zai tsagaita.

Ya cigaba da cewa: “ A cikin wannan sabon tsarin, wasu daga cikin daliban za su rika yin karatunsu da safe inda sauran daliban za su rika yin karatun yamma.

“ Na riga da na kai rahoton wannan al’amari zuwa ga ma’aikatar SUBEB dake Dutse. Na kuma miqa roko na ga SUBEB da kuma majalisar karamar hukumarmu da suyi kokarin cike filin makarantar da qasa.”

Wasu manema labarai da suka samu zuwa ganin makarantun sun bayyana mana cewa ruwa ya cika azuzuwa maqil tun daga sama har qasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel