Da dumi dumi: Yan Shia suna gudanar da zanga zanga a garin Kaduna

Da dumi dumi: Yan Shia suna gudanar da zanga zanga a garin Kaduna

Mabiya mazhabar Shia sun fara gangamin zanga zanga a garin Kaduna, kamar yadda suka yi a babban birnin tarayya Abuja, da kuma jahar Legas, a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan shian sun fara zanga zangar ne da misalin karfe 2 na rana a kan titin Jos dake cikin gari, amma kafin a ankara sun mamaye titunan Kano da kuma Kontagora har ma babbar kasuwar garin Kaduna.

KU KARANTA: Mace mai dauke da juna biyu da kananan yara 2 sun mutu a ambaliyan ruwa a Filato

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa yan Shi’an suna gudanar da zanga zangar ne don nuna bacin ransu da cigaba da rike jagoransu Malam Ibrahim Zakzaky da gwamnatin Najeriya ta kama tun shekaru 4 da suka gabata.

A yayin da yan Shi’an suka fara gangamin, sai labari ya fara yaduwa a cikin gari, kafin kace kule jama’a sun fara guje guje, yayin da yan kasuwa masu shaguna suka fara garkame shagunansu cikin hanzari saboda tsoron abinda ka iya faruwa.

Shima wanda ganau ba jiyau ba, Badamasi Aliyu yace yan Shi’an sun taru dayawa, wanda hakan ya tsoratar da jama’a, amma daga bisani jami’an Yansanda sun dakile zanga zangar, tare da kwantar da hankulan jama’a.

A wani labarin kuma jami’an rundunar Yansandan Najeriya sun yi fama da mabiya mazahabar Shia a yayin da suka gudanar da wani gangamin zanga zanga a babban birnin tarayya Abuja, wanda har ta kai ga sun yi amfani da barkonon tsohuwa.

Yan shia’an suna gudanar da zanga zanga ne da nufin neman gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sako musu jagoransu, Ibrahim Zakzaky tare da matarsa. yan shia’an sun yi shirin yin zaman dirshan a dandalin Eagle Square ne, amma sai Yansanda sun ci musu birki.

Daga bisani Yansanda sun gayyaci jagororin zanga zangar, Nura Marafa da Mujahid Muhammad su fito su tattauna dasu, amma fitarsu keda wuya Yansandan suka shiga marinsu tare da jibgarsu, daga nan kuma suka yi awon gaba dasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel