Mace mai dauke da juna biyu da kananan yara 2 sun mutu a ambaliyan ruwa a Filato

Mace mai dauke da juna biyu da kananan yara 2 sun mutu a ambaliyan ruwa a Filato

Akalla mutane uku ne suka rigami gidan gaskiya a sakamakon wani ambaliyan ruwan da aka samu a dalilin ruwan sama daya sauka kamar da bakin kwarya a jahar Filato, inji rahoton jaridar The Sun.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito lamarin ya auku ne a karamar hukumar Jos ta Arewa, inda ta bayyana sunayen wadanda suka mutu a sanadiyyar ambaliyan kamar haka; Hauwa Bello yar shekara 6, Binta Jafaru yar shekara 54 da kuma diyarta Fatima Jafaru mai shekaru 5.

KU KARANTA: Yan Shia sun ji a jikinsu yayin wata sabuwar arangama da suka yi da Yansanda a Abuja

Ambaliyan ya auku ne a ranar Laraba, 10 ga watan Yuli sakamakon rashin kyakkyawan hanyar ruwa a gaban wani kango, wanda hakan yasa katangar kangon ya fadi a kan Binta da diyarta Fatima yayin da suka fake a kangon bayan sun fito daga ziyarar gidan yayanta.

Sanatan mazabar Filato ta Arewa, Istifanus Gyang wanda ya samu wakilcin Daniel Dem ya kai ziyarar jaje ga iyalan mamatan, tare da kai musu tallafa musu da kayan agaji, sa’annan ya gargadi jama’an yankin da su lura da ambaliyan ruwa da ake samu a yankin.

“Bamu ji dadin abinda ya faru anan ba, an samu ambaliyan ruwa kuma mutane sun mutu, Sanata Gyang ya samu labarin abinda ya faru, don haka ya wakiltani na wakilceshi wajen jajanta ma jama’an tare da isar musu da kayan tallafi.

“Haka zalika ya aikoni da kudi na kawo ma iyalan wadanda abin ya shafa domin su fara sabon ginin gidajensu da ruwan ya lalata. Muna godiya ga Allah da Ya tseratar da rayuwar wani karamin yaro dan shekara 6 wanda aka garzaya dashi asibiti, an duba lafiyarsa kuma har an sallameshi.” Inji shi

Daga karshe ya yi fatan lamarin ba zai kara faruwa a yankin ba, sa’annan ya kara da kira ga jama’a dasu dinga buda ma ruwa hanya ta hanyar gyara kwatocinsu da lambatu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng