Kasar Canada za ta karbi bakuncin gwamnonin arewacin Najeriya

Kasar Canada za ta karbi bakuncin gwamnonin arewacin Najeriya

-Gwamnonin arewa za su gudanar da taron kwana biyu a kasar Canada

-Taron na kwana biyu da za gudanar a kasar Canada cikin watan Agusta zai taimaka sosai wajen magance matsalolin yankin arewa kuma zai bude hanyoyi da dama da za a habbaka tattalin arzikin yankin

Gwamnonin arewa sun shirya tsaf don gudanar da taron kwana biyu da za a yi a ranar Alhamis da Juma’a, 1 zuwa 2 ga watan Agusta na wannan shekarar a kasar Canada inda za su tattauna akan harkar ilimi, ma’adanai, harkar noma da harkar kiwon lafiya.

Babu shakka, arewacin Najeriya ta sha fama sosai da matsalolin ta’addanci daga yan kungiyar Boko Haram. Hare haren Boko Haram ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyi da dama da wajajen more rayuwa na al’umma wanda hakan ya kawo ci baya sosai a yankin na Arewa.

Jihohin Borno, Zamfara, Katsina, Adamawa, Bauchi, Taraba, Gombe da Yobe ne suka fi fuskantar matsalolin ta’addanci daga wajen yan kungiyar Boko Haram da yan bindiga wanda hakan ya sanya mutane da dama suka rasa gidajen zamansu suke zaune a sansanonin yan gudun hijira.

Haka zalika takaddamar siyasa da cin hanci da rashawa na daya daga cikin abubuwan da suka mayar da yankin arewa ya zama koma baya a arewacin Najeriya musamman harkar samar da kiwon lafiya.

KARANTA WANNAN: Akwai alamun Fashola, Amaechi da Onu za su rike mukamansu

Bugu da kari, arewacin Najeriya na fama da karancin mutanen da ke shiga makarantun zamani, wanda hakan ya kara taimakwa wajen mayar da yankin koma baya a Najeriya, kasancewar ilimi shine gishirin zaman duniya, wanda kuma shine babban makamin da za a canza duniya da shi.

Taron na kwana biyu da za gudanar a kasar Canada cikin watan Agusta zai taimaka sosai wajen magance wadannan matsalolin kuma zai bude hanyoyi da dama da za a habbaka tattalin arzikin jihohin arewa da samar da gine gine idan har gwamnonin arewan za su dage wajen samar da ilimin firamare da sakandare kyauta su kuma tilasta karatun ga yara.

Ana sa ran za a tattauna duka wadannan abubuwan a taron na Canada.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel