‘Yan sanda sun damke yan ta’dda 35 a Katsina tare da kwato wasu muggan makamai

‘Yan sanda sun damke yan ta’dda 35 a Katsina tare da kwato wasu muggan makamai

- Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta yi nasarar damke 'yan ta'dda 35 tare da kwato makamai guda 36

- Kwamishinan yan sandan jihar Katsina shi ne ya shaidawa manema labarai wannan batu inda ya ce a tsakanin watan Yuni zuwa Yuli ne akayi wannan gagarumin kame

- Kari a kan makamai da aka kwato akwai dabbobi irin su shanu, tumaki da awaki da aka karbe

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar damke mutum 35 da laifuka daban-daban da suka kunshi garkuwa da bil adama, fashi da makami da kuma sace-sace.

Da yake jawabi a kan kama yan ta’addan, Kwamishinan yan sandan Katsina, Sanusi Buba ya ce, rundunarsa ta samu nasarar kwato makamai guda 36 a tsakanin watan Yuni zuwaYuli.

Kwamishinan ya bayyana wa manema labarai cewa, hadin kai da kuma goyon bayan mazauna al’ummomin da abin ya fi shafa zai taimaka wa jami’an ‘yan sanda kwarai da gaske wurin kawo karshen ayyukan ta’addanci a jihar.

Daga cikin makaman da rundunar ‘yan sandan ta samu nasarar karbewa akwai; bindiga kirar AK47 guda 14, bindiga kirar LAR daya, fisto daya da kuma dobul baral guda shida.

KU KARANTA:Rikicin ‘yan shi’a: Sufeto janar na ‘yan sanda ya ziyarci jami’an da aka raunana a Asibiti (Hotuna)

Bugu da kari, akwai harsashin bindigogin mai yawan gaske da aka samu nasarar kwacewa. Akwai kuma shanu guda talatin da biyu, tumaki guda 13 da kuma awaki guda 3.

A wani labarin mai kama da wannan kuwa, zamu ji cewa, Sufeto janar na yan sandan Najeriya ya kai ziyara Asibitin Kasa dake Abuja domin duba jami’an yan sandan da yan shi’a suka raunata a Majalisar dokoki ranar Talata.

Sufeto janar, Muhammad Adamu ya ziyarci asibitin ne domin gaisuwa da kuma jaje ga jami’an da wannan al’amari ya rutsa da su, inda ya bada tabbacin cewa hukumar yan sanda zata biya duka kudin magungunansu, yayin da kuma ake cigaba da gudanar da bincike kan wadanda suka aikata wannan mummunan aiki. A halin yanzu dai an kama mutum 40 kamar yadda Sufeton ya fadi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel