NAHCON za ta gina wa maniyyatan Kano katafaren Otel mai dakunna 500

NAHCON za ta gina wa maniyyatan Kano katafaren Otel mai dakunna 500

Hukumar Aikin Hajji Ta Kasa (NAHCON) ta ce za ta gina otel mai dakuna 500 a garin Kano domin ya zama masauki ga maniyyatan jihar da ke jiran lokacin da jirgin su zai tashi domin zuwa kasa mai tsarki.

Shugaban NAHCON, Abdullahi Mukhtar ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da ya ke duba kayayakin da hukumar ta tanada domin aikin jigilar maniyyatan wannan shekarar da za a fara a kasar daga jihar Kano.

Ya ce gina otel din yana da matukar muhimmanci saboda akwai bukatar a bawa maniyyatan masauki mai kyau kafin su hau jirgi a filin sauka da tashin jirage na Mallam Aminu Kano, MAKIA.

DUBA WANNAN: An kama wasu mata 4 dumu-dumu suna madigo a Kwallejin Kimiyya a Kebbi

Mista Mukhtar ya kara da cewa za a cigaba da amfani da otel din bayan kammala aikin hajjin domin hukumar ta rika samun kudin shiga da za ayi amfani da shi wurin kulawa da otel din.

Shugaban ya kuma ce NAHCON tana gina asibiti a sansanin maniyyatan a garin Kano wadda ya ce an kusa kammalawa.

A cewarsa, asibitin za yi amfani ga maniyyatan da ke da bukatar a duba lafiyarsu kafin su bar Kano domin zuwa kasa mai tsarki.

Ya ce: "Mun yanke shawarar gina otel din ne saboda muna son maniyyatan mu samu ingattacen kulawa kuma su san walwala da jin dadinsu na da muhimmanci a gare mu.

"Irin otel din da za mu gina zai dace da su. Muna son su samu masauki mai kyau a maimakon su rika sauka a sansanin maniyyata."

Daga karshe ya yi kira 'yan Najeriya su zama wakilai na gari idan su tafi kasar Saudiyya su guj aika wani abu da zai iya bata sunar Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel