Za a samu sabuwar Boko Haram idan ba a saki El Zakzaky ba - Majalisa ta fadawa FG

Za a samu sabuwar Boko Haram idan ba a saki El Zakzaky ba - Majalisa ta fadawa FG

Mambobin Majalisar Wakilai na Tarayya sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi biyaya ga umurnin na sakin shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) Sheikh Ibrahim El Zakzaky.

A zaman da majalisar tayi a ranar Laraba, 'yan Majalisar sun ce zanga-zangar rashin amincewa da tsaron shugaban su da 'Yan Shi'an ke cigaba da yi kan iya haifar da fitina.

An tsare El Zakzaky ne bayan da 'yan kungiyar su kayi arangama da tawagar Shugaban hafsoshin kasa na Najeriya, Tukur Buratai a shekarar 2015.

Kotu daban-daban sun bayar da umurnin bayar da belinsa amma gwamnatin ta cigaba da tsare shi wanda hakan ya sa mabiyansa suka yi kutse a Majalisar Wakilai na Tarayya a ranar Talata.

DUBA WANNAN: An kama wasu mata 4 dumu-dumu suna madigo a Kwallejin Kimiyya a Kebbi

A yayin zaman majalisar, shugaban marasa rinjaye, Ndudi Elumelu ya gabatar da wata kudiri na kira ga takwarorinsa su gudanar da bincike kan lamarin da kuma kara inganta tsaro a majalisar.

Yayin da wasu 'yan majalisar suka goyi bayan inganta tsaron wasu sun jadada cewa ya dace a binciko ainihin matsalar wadda itace cigaba da tsaren El-Zakzaky.

Sun bayyana cewa irin wannan lamarin ne ya haifar da kungiyar Boko Haram a Najeriya.

Onofiok Luke daga Akwa Ibom ya ce abin takaici ne yadda gwamnatin tarayya ke kin bin wasu dokokin kotu na sakin El-Zakzaky.

"Idan har kotu ta ce a sake shi, ya kamata mu bukaci gwamnati ta sake shi. Ba batun kutsen da akayi a majalisa bane abinda ya kamata mu rika tattaunawa."

Bamidele Sam daga jihar Osun ya ce cigaba da tsare El Zakzaky rashin adalci ne kuma idan aka yi wa mutum daya rashin adalci abin ya shafi kowa.

"Ina kira da gwamnatin tarayya da sake duba batun shugaban kungiyar ... ta bari doka ya yi aikinsa ... domin kaucewa samuwar sabuwar Boko Haram daga kungiyar Shi'a," inji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel