Na kashe masoyiyata ne saboda ta hana ni saduwa da ita - Saurayi

Na kashe masoyiyata ne saboda ta hana ni saduwa da ita - Saurayi

Wani saurayi mai shekaru 26, Bidemi Mojupa da ake zargi da kashe masoyiyarsa a cikin unguwar rukunin gidajen Corporation da ke Amuwo Odofin a ranar Talata da ta gabata bai nuna wata alamar nadama ba.

Cikin yanayi na rashin nuna nadama kan abinda ya aikata, matashin ya yi ikirarin cewa bai yi niyyar kashe 'abokiyar saduwarsa' ba mai suna Christy amma rashin yarda ta sadu da shi ne yasa ya kashe ta.

"Wukan kitchen na caka mata. Bata san zan aikata hakan ba. Nayi amfani da wukar na bare lemu kuma na ajiye kan na'urar wanke tufafi kafin in tafi in dako ta.

"Bayan kashe ta, tsoro ya kama ni kuma na so in gudu. Ban san yadda zanyi da kai na ba," inji shi.

DUBA WANNAN: Shaidan Atiku da PDP ya basu kunya a gaban kotu

Mojupa wanda ya kammala karatunsa a fanin koyan aikin jarida daga Polyteknik na jihar Rivers ya ce wannan ba shine lokaci na farko da suka saba saduwa ba inda ya ce ya tura ta cikin gida da karfi da yaji ne kuma ya caka mata wuka a wuya.

A cewarsa, ya yi tatul da wata kwaya mai suna Rohypnol da ya koya shan ta a lokacin da ya shiga kungiyar 'yan asiri ta Vykings a makaranta wacce karfin ta ya data valium sau 10.

Wanda ake zargin da 'yan sanda suka yi holensa a Yaba a ranar Talata ya ce ya matsu da son saduwa ne kuma ransa ya baci bayan Christy ta ki amincewa da shi.

Mojupa ya ce ya yi yunkurin tilasta mata amma ta ki inda ta ce sai ya biya ta kudi kafin ta amince masa wanda hakan ya yi sanadiyar barkewar rikici tsakaninsu wanda hakan yasa makwabta suka leko domin duba abinda ke faruwa.

Wanda ake zargin ya musanta cewa asiri zai yi da ita kamar yadda ya fadi a wani bidiyo da ke yawa a kafafen sada zumunta inda ya ce dukkan da akayi masa ne yasa ya amsa hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel