Shan giya haramun ne a jihar Jigawa: Hukumar Hizbah ta damke mutane 48, kwalayen giya 37

Shan giya haramun ne a jihar Jigawa: Hukumar Hizbah ta damke mutane 48, kwalayen giya 37

Hukumar dabbaka shari'ar Musulunci, Hisbah, a Jigawa ta damke mutane 48 da kwalayen barasa 37 a karamar hukumar Taura na jihar.

Kwamandan hukumar, Ibrahim Dahiru, ya bayyana hakan ga manema labarai ne ranar Talata, 9 ga wtaan Yuli, 2019.

Kwamanda Dahiru ya ce an damke wadannan masu giyan ne tare da jami'an yan sanda a wani harin bazata da suka kai kauyen Gugunju.

Ya bayyana cewa an damke mata 30 da ake zargi da aikin karuwanci tare da mazaje 18 kuma za'a mikasu ga hukuma domin kaddamar da bincike da ladabtar da su ba.

Kwamanda Dahiru ya yabawa mazaunan kauyen, musamman matasa, wadanda suka taimaka wajen gudanar da wannan aiki.

KU KARANTA: Cin zarafin matar Aure: Sanata Elisha Abbo ya gurfana gaban majalisa

Yace: "Muna shawartan al'umma su daina aikata abubuwan kunya da za su gurbata tarbiyyar al'umma. Ba zamu gushe muna yakan wadannan abubuwa ba musamman shan giya."

"Bugu da kari, muna tunatar da mutane cewa shan giya haramun ne a dukkan sassan jihar nan."

A labari mai kama da haka, Hukumar Hisban jihar Jigawa ta damke yan gidan magajiya 14 kuma sun garkame kwalaben barasa 100 a garin Kazaure, hedkwatan karamar hukumar Kazaure.

Hisbah, hukuma ce da aka kafa domin dabbaka shari'ar addinin Musulunci iya gwargwado a jihar Kano da Jigawa.

Kwamdandan hukumar na jihar, Ibrahim Dahiru, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin, 20 ga watan Mayu, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel