Dubu ta cika: An kama likitan karya a Jihar Adamawa

Dubu ta cika: An kama likitan karya a Jihar Adamawa

-Jami'an hukumar NSCDC sun damke wani mutum mai ikirarin likitancin karya a jihar Adamawa

-Mutumin mai suna Imuere Ejiro ya fadi da bakinsa cewa an taba kama shi a jihar Legas amma sai dai ya ce rashin lasisi ya sanya aka kama shi a wan can lokaci

-Kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya reshen jihar Adamawa, Nuraddeen Abdullahi ne ya bamu wannan labari

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya wato NSCDC a jihar Adamawa ta samu nasarar damke wani mutum wanda ke ikirarin cewa shi likitan ido ne a Yola.

Da yake bada wannan labari ga manema labarai, Kwamandan hukumar a jihar, Mista Nuraddeen Abdullahi ya ce wanda aka kaman mai suna Imuere Ejiro ya kasance yana duba marasa lafiya a asibitocin kudi guda biyu a Yola.

KU KARANTA:Da zafinsa: ‘Yan majalisa 14 na Edo sun tunkari Majalisar dokoki da neman a sake zaben shugabancin majalisar jiharsu

Abdullahi ya ce, an kama wannan mutumin tare da fotokofin takardun kaninsa wadanda yake amfani da su a matsayin nashi.

Kwamandan ya cigaba da cewa, an taba kama wannan mutumin a Legas inda Kungiyar rajistar likitocin ido ta Najeriya ta kama shi tare da cinsa tarar naira dubu dari biyu (200,000).

Kwamandan yayi amfani da wannan damar domin yin kira ga jami’an tsaro kan cewa su sanya idanu a kan irin wadannan miyagun mutane.

Abdullahi ya cigaba da cewa: “ Hukumar NSDC ta tura da masu leken asiri daga cikin jami’anta cikin kauyuka domin samo bayanai kan rikicin manoma da makiyaya a Adamawa."

Shi kuwa Ejiro cewa yayi: “ Ni fa ba likitan bogi bane, kama nin kuma da akayi a Jihar Legas ya kasance ne a sanadiyar aiki babu lasisi inda aka nemi na biya N255,000 kuma na fara biyan N65,000 zuwa ga kungiyar amma ban kammala ba.”

Har ila yau, zance daga bakin reshen kungiyar ta likitocin ido na jihar Adamawa wanda muka samu daga bakin shugabanta, Dakta Okafor Ikechukwu yace “ karya wannan mutumin yake yi ba likita bane shi.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel