Wata matashiya Asmau Haruna ta bata bayan ta bar gidansu a Kaduna zuwa Kano

Wata matashiya Asmau Haruna ta bata bayan ta bar gidansu a Kaduna zuwa Kano

Wata mai amfani da shafin zumunta mai suna @milaaabm ta koka a shainta inda ta yi kira ga ma’abota amfani da shafin da su taimaka wajen taya ta neman kanwarta.

A cewar @milaaabm, kanwar tata mai suna Asmau Haruna, ta bata kimanin kwanaki hudu da suka gabata. Ta kara da cewa matashiyar ta yi tafiya ne daga gidansu da ke Kaduna a ranar Juma’a, 5 ga watan Yuli zuwa Kano.

Sai dai kuma tunda ta sanya kafa ta bar gida, ba a sake ganinta ba.

Da take wallafa lamarin a shafin twitter tace: “Dan Allah ku tayani watsawa. Wannan kanwata ce Asmau aruna, ta bata tsawon kwanaki hudu kenan. Ta bar gida daga (Ladduga, karamar hukumar Kacia, jihar Kaduna) a ranar Juma’a zuwa Kano. Idan kana da wani bayani dan Allah a kira 08033519140 08032701203."

KU KARANTA KUMA: Saurayi dan shekara 14 ya shiga hannu da laifin fyade a kasar Jamus

A wani labari na daban, mun ji cewa Cibiyar yaki da garkuwa da mutane reshen hukumar 'yan sandan jihar Imo, ta samu nasarar cafke wani matashi dan shekaru 29, EmManuel Sunday, bisa laifin kulla kutungwila da wasu mutane biyu wajen yin garkuwa da surukin sa mai shekaru 88 a duniya, Pa Njoku Louis.

Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya DCP Frank Mba ya bayyana yayin ganawa da manema labarai a ranar Lahadi, ya ce Emmanuel ya yi hadin baki da diyar dattijon mai shekaru 19, Chinaza Nwogu da kuma dan sa wajen aikata wannan muguwar ta'asa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, miyagun mutanen uku sun yi nufin amfani da kudin fansar wannan dattijon domin gudanar shagalin bikin Emmanuel da kuma Chinaza.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel