Yaran mota 3 sun yiwa barawon waya dukan tsiya har lahira

Yaran mota 3 sun yiwa barawon waya dukan tsiya har lahira

A ranar Litinin, wani babban kotun jihar Legas dake Igbosere ta gurfanar da wasu yaran mota da suka daure wani matashi mai suna, Nse-Obong Idodo, kuma sukayi masa dukan tsiya kan laifin satar waya.

Mai bada shaida a kotu, Roland Ayeme, ya bayyana hakan ne yayinda yake bada shaida a gaban Alkali inda ya laburta cewa a gabansa yaran motan suka lallasa matashin.

Yaran motan uku sune Bashiru Salami, Omokehinde Abdulatif da Ibrahim Ajibola.

Gwamnatin jihar Legas, ta shigar da su kotu kan laifin kisan kai. Lauyan gwamnati, Babatunde Sunmonu, ya ce sashen binciken tashar jirgin ruwa Apapa ne ta bashi aikin.

KU KARANTA: Atiku ya lallasa Buhari a Katsina - Wani shaida ya laburtawa kotun zabe

Ya ce wannan abu ya faru ne ranar 7 ga Yunin 2016 misalin karfe 2 na dare a tashar jirgin ruwan Tin Can, Apapa, Lagos.

Mai bada shaidan ya ce lokacin da ya garzaya wajen da abin ya faru, jami'an yan sanda sun kai gawar mamacin asibitin Mainland dake Apapa.

Ya laburtawa kotu cewa yayinda ake gudanar da bincike, jami'an yan sanda sun gano cewa sai da aka daureshi da igiya kafin sukayi masa duka har ya mutu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel