‘Yan fashi sun aikata mummunan ta’adi a Suleja

‘Yan fashi sun aikata mummunan ta’adi a Suleja

-Wasu 'yan fashi sun kai farmaki Kasuwar IBB dake Suleja a jihar Neja

-'Yan fashin sun fasa shuguna guda hudu tare da dibar kudaden da ba a san adadinsu ba daga cikin shuguna uku

-Yayin gudanar da wannan aika-aika mutum mai-gadi daya ya mutu inda aka bar wani daya da rauni a kafarsa

Wani gungun ‘yan fashi a daren Asabar sun kai farmaki kasuwar IBB dake Sulejan jihar Neja inda suka kashe daya daga cikin ‘yan sintirin dake gadin kasuwar kana suka raunata wani mutum guda.

Kwamandan ‘yan sintirin shiyyar Daudu-gyara inda wannan lamari ya auku, Muhammad Sani Aliyu ya shaidawa wakilin Daily Trust cewa, ‘yan fashi sun fasa shaguna hudu wadanda suka kunshi shuganan: shinkafa, na fulawa, na kayan masarufi da kuma shagon dinki.

KU KARANTA:Mutumin da matarsa ta dabawa wuka ya samu lafiya, ya nunawa bidiyon tsairaci da matarsa ke tura wa samarinta

Ya bayyana cewa, yan fashin sun yi nasarar diban kudaden da ba’a san adadinsu ba daga shaguna uku saboda sun gagara fasa akwatin ajiyar kudin dayan shagon.

Sani Aliyu ya sake cewa, da misalin karfe 3 na dare labarin wannan ta’adi yazo masa. Zuwansa wurin ke da wuya sai ya tadda daya daga cikin jami’ansa kwance a kasa shame-shame da rauni a kafarsa guda daya.

Kamar yadda Sani Aliyu ya ce: “ Nayi kokarin taimakonsa amma daya daga cikin ‘yan fashin yayi amfani da fitila ya haske mani ido. A nan na nemi wani wuri na buya ban kuma fitowa ba sai da naji dayansu na fadin cewa lokacin da aka basu domin yin wannan aikin ya cika, don haka su zo su tafi.

“ Bayan na tabbata sun bar wurin ne na fito. Nan take na kira shugabanmu Alhaji Adamu Landan wanda yayi gaggawar zuwa wurin inda bayan ya iso muka sake ganin gawar wani jami’inmu mai suna Sabiu Abdullahi wanda yan fashin suka kashe.

“ A nan take muka garzaya da wanda ya samu rauni Babbar Asibitin Suleja tare da jami’an yan sanda wadanda suka zo wurin jim kadan bayan lamarin ya auku."

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel