Yansanda sun kama babban limamin daya dirka ma yarinya yar shekara 15 ciki

Yansanda sun kama babban limamin daya dirka ma yarinya yar shekara 15 ciki

Wani babban limamin coci, Pope Paul dan shekara 42 ya dirka ma wata karamar yarinya yar shekara 15 ciki ta hanyar yi mata fyade akai akai a gidansa dake Egan, cikin unguwar Igando na jahar Legas.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wannan mugun limamin coci ya samu damar yi ma karamar yarinyar fyade ne sakamakon zaman da take yi a gidansa a matsayin yare aiki tun a shekarar 2017.

KU KARANTA: Zan farfado da duka matatun man Najeriya 4 kafin 2023 – Mele Kyari

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Legas, Elkana Bala ne ya bayyana haka a ranar Litinin, 8 ga watan Yuli, inda yace mahaifiyar yarinyar ce ta taso tun daga garin Akure na jahar Ondo ta kai musu kara a ranar 2 ga watan Yuli na shekarar 2019.

“Da misalin karfe 3 na rana mahaifiyar yarinyar ta kai karar Faston a ofishin Yansanda inda tace Faston dake zama a gida mai lamba 10/11 titin Aminu a unguwar Igando yana kwanciya da diyarta yar shekara 15 tun tana da shekara 12.” Inji shi.

Kaakaki Elkana yace tuni suka kama wannan babban limamin coci, kuma zasu gurfanar dashi gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.

Haka zalika, kaakakin ya bayyana cewa Yansanda sun kama wani tsohon najadu dan shekara 68 mai suna Yisah Showunmi da laifin yi ma diyarsa mai shekaru 15 fyade, sai dai tsohon bai tsaya nan ba, hatta kawayen diyar tasa bai bari ba, inda aka tabbatar da cewa yana musu fyade su ma.

A wani labarin kuma, Yansandan jahar Imo sun samu nasarar kama wani matashi daya hada baki da budurwarsa da yayanta inda suka yi garkuwa da mahaifin budurwar dan shekara 88 da nufin su karbi kudin fansa domin su gudanar da shagalin aurensu da kudin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel