Adamawa za ta gudanar da zaben kananan hukumomi

Adamawa za ta gudanar da zaben kananan hukumomi

-Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Adamawa ta bayyana cewa za ta gudanar da zaben kananan hukumomi a cikin watan Nuwamba

-Shugaban hukumar, Isah Shettima ne ya bayyana haka

-Shettima ya kuma bayyana cewa za a fara gudanar da kamfen a ranar 10 ga watan Yuli 2019

A jiya Litinin 8 ga watan Yuli 2019, hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Adamawa ta bayyana tsarinta na gabatar da zaben kananan hukumomi a cikin watan Nuwamba na wannan shekarar.

A jawabin da shugaban hukumar, Isah Shettima ya fitar ga manaima labarai, hukumar ba ta bayyana takamaimai ranar da za ta gudanar da zaben ba.

Shettima ya bayyana cewa “Za a fadi takamaimai ranar da za a yi zaben nan da ba da dadewa ba. A saboda haka jam’iyyun da ke da bukatar gabatar da dan takara a zaben, sai su fara shirin kamfen da za a fara a ranar 10 ga watan Yuli 2019.”

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Sarkin Kano ne ya tunzura matan arewa suke kashe mazajensu - Hon. Zulyadaini Sidi Karaye

Ya kara da cewa “Haka zalika, za a gudanar da zaben fidda gwani daga 31 ga watan Agusta zuwa 7 ga watan Satumba 2019 sa’annan a gabatar da sunayen yan takara da sukayi nasara ga hukumar kafin ranar 10 ga watan Oktoba 2019.”

Gwamna Ahmadu Fintiri ya aikawa majalisar dokoki ta jihar Adamawa kudiri inda ya bukaci da a kafa kwamitin gudunarwa a kananan hukumomi 21 na jihar.

A ranar 25 ga watan Yuni 2019, majalisar ta amince da kudirin inda daga bisani gwamnan ya kaddamar da kwamitocin a ranar 4 ga watan Yuli 2019.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel