Ayi hattara: Ciwon Zuciya ya kusa kama duk mai aikata abubuwan da wani Masani ya fada

Ayi hattara: Ciwon Zuciya ya kusa kama duk mai aikata abubuwan da wani Masani ya fada

- Lafiyar ita ce jarin Mutum, ga duk mai wayo

- Wasu Kwararru sun bayyana wasu sirrika da kan iya zama rigakafin kamuwa da ciwon Zuciya

- Sai dai da yawan Mutane ba su san wadannan sirrika da alamomin ciwon Zuciyar ba

Wani kwararren masanin lafiyar Zuciya Farfesa Ibrahim Adeola-Katibi daga Asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin (UITH) ya ja hankalin ‘yan Najeriya bisa wasu abubuwa da suke aikatawa wanda kan saurin sanya kamuwa da ciwon Zuciya cikin sauki.

Farfesa Katibi yayi jan hankalin ne a yau Lahadi yayin gabatar da wata mukalarsa mai taken “Ciwon Zuciya: Alamomi da yanayinsa, hanyar kariya da tsayar da shi” a yayin wani taron gabatar da lekcoci na watan Azumin Ramadan da kungiyoyin yada addinin Musulunci (IMAN) suka shirya.

Abubuwa masu sauki da Mutane keyi dake haddasa ciwon Zuciya
Abubuwa masu sauki da Mutane keyi dake haddasa ciwon Zuciya

Kwararren Likitan shawarci ‘yan Najeriya da su gujewa cin abinci da yawa barkatai da Shaye-shaye da kuma shan Giya, domin gujewa sagegeduwa da lafiyarsu.

Sannan kuma ya kara shawartar Mutane da su riki al’adar zuwa ganin Likita akai-akai domin duba lafiyarsu don gujewa matsala.

KU KARANTA: Wani dan majalisa kuma na hannun daman gwamna Wike ya fita daga PDP, ya koma APC

Shi ma ana sa jawabin Dr Abdulwasiu Yusuf daga dai Asibitin na UITH cewa yayi ,

Daga cikin abubuwan da kan sanya kamuwa da ciwon Zuciya akwai cin abinci mai dauke da kitsen da yake wahalar narkewa (Cholesterol) da ciwon Sukari da Hawan Jini da Aiki ba kakkautawa ba tare da hutu ba da kuma Kiba mai yawa da sauransu.

Dr Yusuf ya kuma bayyana cewa ana iya magance ciwon na zuciya ta hanyar magunguna ko kuma fida. Amma daga cikin alamomin da ya kamata a lura da su na bugawar Zuciya sun hada da; Ciwon kirji mai zafi da ka iya watsuwa har zuwa kafada, hannu da kuma wuya.

Sannan ya kuma cewa wadannan alamomi ka iya janyo yin amai da kuma fitar numfashi a kyar da tari da juwa tare da faduwa haka kawai.

Ayi hattara: Ciwon Zuciya ya kusa kama duk mai aikata abubuwan da wani Masani ya fada
Ayi hattara: Ciwon Zuciya ya kusa kama duk mai aikata abubuwan da wani Masani ya fada

A don haka ne ya bukaci jama’a da su rinka motsa jikinsu akai-akai su kuma rinka shan ‘ya’yan itatuwa masu gina jiki da kuma samun isasshen hutu tare da bacci.

Ana sa jawabin Shugaban Kwalejin lafiyar UITH na Jam’iar Ilorin Farfesa Abdulwahab Johnson, kira yayi ga iyaye da su rika ziryartar asibiti lokaci zuwa lokaci domin duba lafiyar Zuciyarsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel