Yadda aka tilastawa daliba cire hijabi kafin ta shiga makaranta a Ibadan (Bidiyo)

Yadda aka tilastawa daliba cire hijabi kafin ta shiga makaranta a Ibadan (Bidiyo)

Wani bawan Allah ya yi korafin yadda masu tsaron makaranta a garin Ibadan suka tilastawa diyarsa cire hijabinta kafin ta shiga makarantar.

Kamar yadda aka haska a faifan bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, mai tsaron makarantar ya umurci wasu dalibai mata su cire hijibinsu kafin su shiga makarantar.

Mai tsaron makarantar ya ce "Ku cire hijabin, idan kun fito daga harabar makaranta sai su saka. Idan kun fita waje babu wanda ke da ikon hana ku saka hijabi."

Wasu mutane da ke tsaye a wurin da abinda ya faru sun goyi bayan mai tsaron makarantar yayin da wata mace ta masa gargadin cewa yana neman rikici ne.

DUBA WANNAN: Kannywood: Adam Zango ya nuna sabuwar babbar mota ta miliyan N23m da ya saya

Daga bisani mahaifin dalibar ya zo kofar makarantar da kansa amma masu tsaron makaranta suka fada masa cewa an basu umurni daga sama ne cewa kada su kyalle dalibai su rika shiga makaranta sanye da hijabi.

Mahaifin daliban ya yi ikirarin cewa mai tsaron makarantar ya samu daurin gindi ne daga wasu ma'aikatan jami'ar Ibadan.

Mahaifin daliban ya koka kan cewa ba dai-dai bane a hana diyarsa shiga makaranta da hijabi duba da cewa ya biya mata kudin makaranta.

Ga dai bidiyon yadda lamarin ya kasance:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel