Gawa ta ki rami: Matashi Mohammed ya mike zumbur bayan an haka kabarun binne shi

Gawa ta ki rami: Matashi Mohammed ya mike zumbur bayan an haka kabarun binne shi

Har an haka kabari, kuma 'yan uwa sun hallara domin binne shi amma sai komai ya canja a wurin taron jana'izar wani mamaci a Indiya.

'Yan uwa da abokan arzikin wani matashi, Mohammad Furqan, sun cika da murna da farin ciki bayan ya farfado daga mutuwar da likitoci suka tabbatar ya yi.

An mayar da matashin, mai shekaru 20, zuwa asibiti bayan ya mike zumbur a daidai lokacin da aka taru domin daukan gawarsa zuwa makabarta, inda aka haka kabarin binne shi.

Batun farfadowar matashin a birnin Lucknow ya girgiza kasar Indiya tare da saka alamar tambaya a kan kwarewar ma'aikatan lafiya na jihar Uttar Pradesh, lamarin da ya saka jama'a yin kiraye-kirayen a gudanar da bincike a kan lamarin.

A ranar Litinin ne wani asibitin kudi ya shaida wa dangin Furqan cewa ya mutu bayan ya shiga dogon suma sakamakon wani hatsari da ya ritsa da shi a ranar 21 ga watan Yuni.

DUBA WANNAN: Magidanci ya kwankwadi 'sniper' bayan ya kama matarsa turmi da tabarya da tsohon saurayin ta

Sun fada wa dangin Furqan cewar ya mutu ne bayan sun fada wa asibitin cewa basu da sauran kudin cigaba da daukan nauyin kula wa da shi.

Mohammad Irfan, yayan Furqan ya ce sun yi matukar girgiza daga abubuwan da suka faru a kan dan uwan na sa.

Ya fada wa wata jaridar kasar Indiya, 'Hindustan Times', cewa "mu na cikin halin juyayin mutuwarsa, har an haka kabarin binne shi sai kawai mu ka ga kafarsa na motsi. Nan da nan mu ka dauki Furqan zuwa asibitin Ram Manohar inda likitoci suka tabbatar mana da cewa ya na da rai, san nan suka saka shi a kan wani gado na musamman mai na'urori."

Narendra Agarwal, babban likita na Lucknow ya ce: "mun san da faruwar lamarin, kuma za a gudanar da cikakken bincike."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel