Yanzu-yanzu: 'Yan Bindiga sun kashe mutane 15 a Katsina

Yanzu-yanzu: 'Yan Bindiga sun kashe mutane 15 a Katsina

- Yanzun nan muke samun rahoton cewa, an kashe mutane 15 a jihar Katsina jiya

- Hakan ya biyo bayan wani hari da 'yan bindiga suka kai wasu kauyuka guda hudu na karamar hukumar Kankara da Danmusa

- Yanzu haka dai mutanen kauyukan sun dunguma zuwa fadar Sarkin Katsina domin jin dalilin da yasa ake kashe su babu gaira babu dalili

An kashe mutane sha biyar a wani hari da 'yan bindiga suka kai kauyuka hudu a karamar hukumar Kankara da Danmusa dake jihar Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigar sun fara kai harin Unguwar Nagwande da misalin 4:30 na yamma, inda suka kashe mutane hudu, daga suka yi gaba zuwa Unguwar Rabo suka kashe mutane tara, daga baya kuma suka sake kai hari Gidan Daji inda suka kashe mutane biyu.

Kauyukan duka suna yankin karamar hukumar Kankara ne.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sunyi awon gaba da wani babban likitin asibitin Malam Aminu Kano tare da 'yan uwansa guda biyu

Aminiya ta bayyana cewa 'yan bindigar sun wuce zuwa kauyen Maidabino dake karamar hukumar Danmusa da misalin 5:10 na yammacin ranar, inda suka bude wuta a cikin kasuwar garin yayin da mutane ke kasuwancin su.

Mutane da yawa sun mutu, inda wasu kuma suka ji muggan raunuka, in ji Aminiya.

A lokacin da ake rubuta wannan rahoton, mutanen kauyukan sun gama dauke gawarwakin, kuma sun dunguma zuwa fadar Sarkin Katsina domin kai kukansu akan lamarin.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya ce mutane 11 ne kawai aka kashe a karamar hukumar Kankara, inda kuma aka sake kashe mutum 2 a kauyen Maidabino.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel