'A kore shi kawai' - Sanatan da ya mammari wata mata a shagon sayar da kayan batsa ya fusata 'yan Najeriya

'A kore shi kawai' - Sanatan da ya mammari wata mata a shagon sayar da kayan batsa ya fusata 'yan Najeriya

Sanata Elisha Abbo, mamba mai wakiltar jihar Adamawa ta arewa, ya fusata 'yan Najeriya a dandalin sada zumunta bayan an nadi faifan bidiyonsa yayin da ya ke cin zarafin wata mata a wani shagon sayar da kayan batsa a Abuja.

Jim kadan bayan kafafen yada labarai sun kwarmata labarin yadda Sanata Abbo ya mammari wata mata don kawai ta yi kokarin hana shi dukan kawar ta, 'yan Najeriya, a gida da ketare, sun fusata tare da yin kiran a hukunta shi a kan abinda ya aikata ga matar.

Wani bangare na masu jin haushin abinda sanata Abbo ya aikata, sun yi kira da a kore shi daga majalisa tare da gurfanar da shi a gaban kotu domin girbar abin da ya shuka.

An nadi faifan sanatan mafi karancin shekaru a majalisar dattijai yayin da ya ke cin zarafin wata mata a wani shagon sayar da kayan batsa a Abuja.

Matashin sanatan ya mammari matar ne bayan ta roke shi a kan ya daina cin mutuncin matar da ta mallakin shagon, wacce sanatan ya yi zargin cewa ta kira shi bugagge kuma ta hantari budurwarsa.

Jaridar Premium Times ta bayyana cewar lamarin ya faru ne ranar 11 ga watan Mayu, kimanin watanni uku bayan an zabi Mista Abbo a matsayin sanata - wata guda kafin a rantsar da sabbin sanatoci a ranar 11 ga watan Yuni.

DUBA WANNAN: Bidiyon Sanatan arewa yayin da ya ke shararawa wata mata mari a shagon sayar da kayan batsa a Abuja

Jaridar, wacce ta ce ta mallaki faifan bidiyon, ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a kan idon jami'in dan sanda da ke tare da sanata Abbo, wanda ta ce maimakon ya hana cin zarafin matar, sai ya yi kokarin kama ta.

Korafin matar ne ya fusata Sanata Abbo har ta kai ga ya na kokarin dukanta, ganin haka ne sai kawarta da ke shagon ta yi masa magana tare da bashi hakuri, amma maimakon hakan ya sanyaya zuciyarsa sai ya kara tunzura tare da sharara mata mari kala-kala.

Washegari matar ta je asibiti inda aka duba lafiyar idanunta da suka kumbura sakamakon marin da ta sha a wurin sanatan.

Premium Times ta ce sanata Abbo bai dauki nauyin kudin magungunan da aka rubutawa matar a asibiti ba, hasali ma ko kulawarsa bai nuna ba a kanta balle ya ji tausayinta.

Sai dai, yanzu sanata Abbo ya shiga tsaka mai wuya bayan 'yan Najeriya, daga kudu da arewa, sun fusata tare da caccakarsa a kan cin zarafin matar, da kuma yin kira ga kungiyoyin kare hakkin mata da na bil'adama da su shiga maganar domin nema wa matar hakkinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng