Assha: An hallaka wani ango da abokanshi guda 7 wajen neman aure

Assha: An hallaka wani ango da abokanshi guda 7 wajen neman aure

-Wani matashi mai suna Luka Yakubu ya rasa ranshi da na abokanshi guda bakwai a garin Borong da ke jihar Adamawa, inda ya je neman auren wata yarinya

-Angon da abokanshi, wanda mafarauta ne na sanye da kayansu na mafarauta da kuma bindigoginsu, wanda hakan ya sanya wasu su kayi zargin sun kawo ma garin Borong hari ne

-Yan sanda sun bayyana cewa na kama wadanda suka aikata kisa

Wasu kauraye a Borong dake a karamar hukumar Demsa ta jihar Adamawa sun hallaka wani angon gobe da abokanshi guda bakwai sa’annan suka jefa gawawwakinsu cikin rafi.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar, Sulaiman Nguroje ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda kuma ya bayyana cewa an kama wadanda suka aikata kisan.

Ya bayyana cewa, wadanda aka kashe, wasu mafarauta ne daga karamar hukumar Ahani kuma sun je Borong don su gana da iyayen yarinyar da angon ke so, amma sai wasu suka bayar da sanarwa cewa sun zo ne da niyyar su kai masu hari.

KARANTA WANNAN: Bincike: Sharrin dake tattare da kwanciyar ‘ruf da ciki’

Ya bayyana cewa “Wasu yan kauyen sun kirawo yan sanda aka tafi da su ofshin. Amma sai wasu mutane suka yi gungu suka kashe mafarautan sa’annan suka jefa gawawwakinsu cikin rafi.’

"Angon, wanda mafarauci ne ya samu rakiyar abokan aikinshi, kuma suna sanye da kayansu na mafarauta rike da bindigoginsu, kuma sun tura an gayama mafarautan Borong cewa suna nan tafe.”

Bincike ya nuna cewa angon mai suna Luka Yakubu ya nemi auren wata yarinya a kauyen kuma ya tafi da abokanshi ne da niyyar a daura masu aure amma suka rasa rayukansu sakamakon kisan gillan da aka yi masu.

Wani Alhassan Danladi, wanda shima abokin angon ne ya tsallake rijiya da baya sakamakon cewa bai sanye da kayanshi na mafarauta. Alhassan ya roki gwamnatin jihar da ta taimakawa iyalen mamatan.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel