Bincike: Sharrin dake tattare da kwanciyar ‘ruf da ciki’
Binciken ya masana kiwon lafiya ya tabbatar da horon da addinin Musulunci ya yi ma Musulmai na kauce ma kwanciyar ruf da ciki, kamar yadda wani kwararren likita, Dakta Fasanu Olaniyi ya bayyana a cikin wannan rahoto.
Dakta Olaniyi ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar Daily Trust, inda yace kwanciyar ruf da ciki da mutane ke yi idan suna karatu, kallon fim ko kuma barci na da matukar hatsari ga lafiyar dan Adam.
KU KARANTA: DSS ta kammala bincike akan sabbin ministocin Buhari 21
Majiyar Legit.ng ta ruwaitoshi likitan yana cewa idan mutum ya yi kwanciyar ruf da ciki, sa’nnan ya dogara gwiwar hannunsa a kasa, hakan zai karkata kwanciyar kashin bayansa, tare da takura ma tsokar baya, wanda hakan ka iya kawo ciwon baya.

Asali: Twitter
“Haka zalika idan mutum ya kwanta a cikinsa dole ne sai ya karkatar da fuskarsa gefe, wanda hakan kuma yana kawo ciwon wuya, suma mata masu juna biyu bai kamata su yi kwanciyar ruf da ciki ba saboda takura ma jariri.
“Haka zalika ba zasu kwanta ta hannun dama ba saboda zai danne jijiyoyin dake kai jini zuwa ga zuciya, kwanciyar da tafi dacewa da masu juna biyu shine ta hannun hagu.” Inji shi.
Sauran matsalolin dake tattare da kwanciyar ruf da ciki sun hada da kawo tsaiko ga tsarin farfasa abinci da sarrafashi a jikin dan Adam, daga nan sai mutum ya fara gudawa.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng