Wa'iyazubillah: An kama samari da 'yan mata su 17 suna zina a daki daya tamkar dabbobi a jihar Yobe
Rundunan yan sanda Najeriya reshen jihar Yobe ta gurfanar da masu laifi takwas bisa zargin yiwa wasu yan mata tara fyade da kuma yiwa wasu ciki a Damaturu.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai, kwamishinan yan sanda jihar Yobe, Sunnomu Abdulmalik yayi magaa ta hannun mataimakin kwamishina yace an kama masu laifin ne bayan bayanai da aka samu daga wasu al’umman dake tallafa ma yan sanda a karkaran.
A cewar mataimakin kwamishinan yan sandan, bayan tambayoyi, masu laifin sun bayyana cewa sun sha saduwa da yan matan da ke talla.
Ya kara da cewa akwai masu keken adaidaita sahu guda biyu; Idris Hassan da Iliyasu Muhammad wadanda rundunar ta kama yayin da take gudanar da aikinta, sai dai ba a kama su da hannu a lamarin ba, sai dai an gano cewa suna amfani da adaidaita sahun ne wajen daukar yan matan zuwa wajen da suke lalatar su.
Yayi kira ga al’umma, musamman iyaye da su sa ma yaransu ido don bincikar shige da ficen su don sanar da yan sanda mafakar masu miyagun dabi’u.
Ya ci gaba da cewa, wasu daga cikin wadanda lamarin ya cika dasu sun yi ciki sakamakon tarayyar da suke yi, an kuma bayyana cewa masu laifin kan basu naira dari uku ne zuwa dari biyar bayan sunyi lalata dasu.
KU KARANTA KUMA: Kotu ta dage sauraron karar da mahukuntan fadar Kano suka shigar kan Ganduje
A wani lamari makamancin haka, yan sandan reshen sun kama wani mai suna Muhammadu Hassan wanda ake zargin saduwa da diyarsa mai shekara ashirin da uku da kuma yi mata ciki.
A cewar jawabin, mutumin ya sadu da diyarsa sau uku bayan ya saka mata kwaya cikin abin sha da kosai wanda sakamakon ma’amalan a halin yanzu cikin yayi akalla watanni biyar.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng