N1.2bn kacal na kashe wajen binne gawa ba N2.3bn ba - Tsohon gwamnan Bauchi
-Tshon gwamnan jihar Bauchi Abubakar Mohammed ya bayyana cewa Naira biliyan 1.2 kacal ya kashe wajen sayen kayan binne gawa ba wai Naira biliyan 2.3 da ake ikirari ba.
-Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin mai taimaka mashi kan harkokin labarai Mukhtar jibril, inda ya bayyana cewa gwamnan ya gaji al’adar sayen kayayyakin binne gawa daga magabatanshi
-Jibril ya kuma bayyana cewa an bada kwangilar sayo kayan a bisa ka’ida
Tsohon gwamnan jihar Bauch Abubakar Mohammed ya ce shi Naira biliyan 1.2 kacal ya kashe wajen sayen kayayyakin binne gawa ba Naira biliyan 2.3 da ake ikirari ba.
Maitaimakama tsohon gwamnan kan harkokin labarai, Mukhtar jibril, ya bayyana cewa gwamnan ya gaji wannan al’ada ta sayen kayen jana’iza daga magabatanshi saboda mahimmancin da aikin ke dashi ga al’umma.
Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi ya tuhumi tsohonn gwamnan da kashe kudi Naira biliyan 2.3 wajen sayen kayan binne gawawwaki a cikin wata biyar.
Jibril ya bayyana cewa an sayi kayan binne gawawwakin a bisa ka’ida kuma yan kwangila na gari aka baiwa aikin siyo kayan.
KARANTA WANNAN: Tirkashi: A karon farko Sheikh Dahiru Bauchi yayi magana akan hana Almajiranci da ake shirin yi
Jibril ya ce “Amsar labaran da ke yawo game da itace da ganyayyaki da aka siyo don binne gawa, muna so mu sanar cewa wannan al’ada gadarta gwamnatin Abubakar ta yi daga magabatansa, duba da yadda aikin ke da mahimmanci musamman ga mutane marasa karfi, shi yasa ya cigaba da yi.”
“Amma aikin, kamar yadda sauran ayyuka suke, an bayar da shi ga yan kwangila na kwarai. A takardun mu tabbatattu, an kashe Naira 1,270,743,520 tun bayan hawanmu amma ba kudin da ake zuzutawa ba har Naira biliyan 2.3 da ake ta yadawa a labarai da niyyar a bata sunanmu.”
“Muna yin gira ga mutanen jiharmu da suyi watsi da wannan labarin kanzon kurege da kuma ayyukan marasa kishin.” A cewarshi.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng