In bakai bani wuri: Yan kato da gora sun kai mutanensu don magance matsalolin tsaro a Kebbi

In bakai bani wuri: Yan kato da gora sun kai mutanensu don magance matsalolin tsaro a Kebbi

-Yan kungiyar kato da gora ta jihar Kebbi ta kai mutanen ta wasu kauyuka da ke fama da matsalolin tsaro don su taimaka wajen magance masalolin

-Shugaban Kungiyar ya bayyana cewa akwai mutanensu 20 zuwa 30 a kowacce wad a fadin jihar

-Ya kuma bukaci gwamnati da ta taimaka masu da makamen yaki da yan ta'addan

Yan kungiyar sa kai ta Najeriya (VGN) ta rarraba mutane 4,500 a kananan hukumomi 21 dake a jihar Kebbi don su taimakawa jami’an tsaro wajen yaki da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro da ake fama dasu a wasu kauyuka na jihar.

A jiya Talata 25 ga watan Yuni 2019, shugaban kungiyar ta jihar, Alhaji lawal Augie, ya bayyanawa yan jarida a Birnin Kebbi cewa sun dauki wannan mataki ne don taimakawa wajen magance matsalolin ta’addanci a fadin jihar.

Ya kara da cewa a kwai bukatar a kara karfafa tsaro a jihar kuma yan kungiyar kato da gora a shirye su ke da su taimakawa jami’an tsaro.

Ya ce “Don samar da zaman lafiya da tsaro a jihar Kebbi, mun kai mutanen mu kananan hukumomi 21 a fadin jihar nan. Akwai mutanen mu 20 zuwa 30 a kowacce wad cikin wad 225 da ake dasu a fadin jiharnan.”

KARANTA WANNAN: Allah wadan naka ya lalace: Ina sayarwa da 'yan ta'adda bindiga N30,000, harsashi kuma N700 - In ji Ayuba

Augie ya kara da cewa kungiyarsu na bukatar tallafin gwamnati da mutanen gari wajen magance matsalolin ta’addanci da mutane ke fama da su.

Ya ce “Yan ta’addan nan na da bindiga AK47. Mu wukake da wasu makamai kirar hannu kawai ke gare mu amma duk da haka tsoranmu suke ji.”

Ya bukaci gwamnati da ta kara ma kingiyar ta kato da gora karfi don su samar da tsaro a jihar. Ya ce “Abin jin dadin shine mafi yawan mutanen mu yan kauyukan ne kuma tsofaffin sojoji ne da yan sanda da DSS,”

Ya yabawa hukumar yan sanda da ta yi hadaka da yan kungiyarsu musamman wajen magance matsalar ta’addanci da wasu laifuffuka a jihar. Ya ce akwai bukatar a kara samun hadin kai tsakanin yan kungiyarsu da jami’an yan sanda indai ana so a sami nasara wajen yaki da ta’addanci.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel