An samu gawar wani tsoho kwance da Buduwarsa a daki a Legas

An samu gawar wani tsoho kwance da Buduwarsa a daki a Legas

Mun samu labari cewa jami’an tsaron ‘yan sanda da ke da alhakin binciken kisan-kai a jihar Legas sun gano gawar wani mutumi mai suna Rasaki Balogun ‘dan shekara 56 da ya mutu a wani gida.

Jami’an tsaron sun samu gawar wannan Bawan Allah ne tare da wata da a ke zargin cewa Masoyiyarsa ce. Jaridar nan ta Daily Trust ce ta bayyana wannan Ranar 24 ga Watan Yuni, 2019.

Wannan abin ya faru ne a Unguwar nan ta Victory Estate a gida mai lamba 16 a layin Taiwo Oke, da ke cikin Garin Ejigbo a jihar Legas. Tun a makon jiya ne a ka kawowa jami'ai kukan wani mutumi.

Kakakin ‘yan sandan jihar Legas, Bala Elkana, ya bayyanawa menama labarai cewa wata Akorede Balogun, watau Mai dakin wannan Mutumi ce ta fara kawo masu kukan mutuwar Mai gidan na ta.

KU KARANTA: Dattijo ya shiga gidan yari bayan yi wa Diyarsa fyade

Elkana ya ce jami’an ‘yan sanda sun samu gawawwakin wadannan mutane ne sharkaf a cikin jini kwance a cikin wani daki. ‘Yan sanda sun ce har yanzu ba su iya gane wacece wannan Budurwa ba.

Jami’in ya ce: “An samu gawar wannan mutumi da kuma wannan Budurwa ne kwance cikin jini. Wannan Bawan Allah ya na zaune ne shi kadai a gidan, yayin da ya bar Iyalinsa a wani wuri dabam.”

“Kawo yanzu, ba mu iya gane wacece wannan mata ba. Marigayin ya dauko wannan mata ne kwanaki 2 da su ka wuce daga wani yanki.” Inji Bala Elkana a madadin rundunar ‘yan sandan.

Kakakin jami’an ya ce: “Jami’an da ke binciken kisan-kai daga shiyyar Yaba za su cigaba da gudanar da bincike kamar yadda Kwamsihinan ‘yan sandan jihar, Zubairu Muazu ya bada umarni.

A karshe mai magana da yawun ‘yan sandan na Legas ya yi alkawari za a gano abin da ya kashe wadannan Bayin Allah.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel