Duniya ta zo karshe: Wani gari da ba a bari mutane suyi sallah sai sun biya kudi

Duniya ta zo karshe: Wani gari da ba a bari mutane suyi sallah sai sun biya kudi

Rahotanni sun kawo cewa kungiyoyin mabiya addinin Islama na gangami domn ganin an basu izinin gina masallaci a birnin Askum da ke kasar Habasha.

Mabiya addinin Kirista a yankin na yiwa birnin kallon kasa mai tsarki saboda a nan ne mahaifar mahaifar sarauniya Sheba wadda aka amabata a cikin littafin Injila.

Hakan yasa shugabannin Kirista suka yi watsi da wannan bukata na Musulmai da ke naman a bari su gina masallaci, sannan sun dauki alwashin cewa da dai su ga wannan rana gara ace sun mutu basa duniya.

Wani babban limamin Kibdawa Godefa Merha ya ce suna kallon birnin Askum mai tsarki, tamkar yadda Musulmai ke kallon birnin Makka.

Ya kara da cewa ''kamar yadda aka haramta gina Coci a birnin Makka da Madina haka mu ma muka haramta gina masallaci a Askum mai tsarki''.

"Aksum waje ne mai cikakken tsarki, ba za mu amince a gurbata mana shi ba", in ji Mista Godefa, wanda shi ne mataimakin majami'ar Our Lady Mary of Zion da ke birnin.

Mabiya addinnin Musulunci da Kirista sun yi amanna da cewa Musulmai ne suka same su a masarautar Aksum, wanda daya ce daga cikin manyan masarautu a duniya.

Musulmai sun isa jim kadan bayan bayyanar addinin Musulunci a shekarar 600AD a matsayin 'yan cirani da suka gujewa kisan gillar da kafiran Makka ke musu a wancan lokacin.

Wani mazaunin birnin mai suna Abdu Mohammed Ali, mai shekara 40, ya ce shekara da shekaru zuriyar gidansu na karbar hayar gidaje ne daga Kirista dan samar da masallacin da za su yi sallah da sauran ibada.

KU KARANTA KUMA: Gaskiya ta yi halin ta a kotun sauraron karar zaben shugaban kasa – inji Buhari

Ya kara da cewa ''muna da masallatai 13 da dukkansu haya muke biya. A duk ranakun juma'a idan mukai kiran sallah ta amfani da lasifika, sai Kiristoci su ce wai mun raina Nana Maryam mahaifiyar Annabi Isa AS''.

Shi ma wani likitan gargajiya Aziz Mohammed, da yake zaune a birnin sama da shekara 20, ya ce a wasu lokutan akan tilastawa Musulmai yin sallah a bainar jama'a ba cikin masallaci ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel