Hukumar EFCC ta kama yan danfara da dankara dankaran motoci
-Hukumar EFCC ta kama wasu yan danfarar 'yahoo yahoo' 27 a jihar Ibadan
-Mukaddashin mai magana da yawun hukuman ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa an kuma kama wasu yan mata hudu da ake tunanin yan matan yan dafarar ne
-Ya kuma bayyana cewa an kwato manyan motoci masu tsada guda takwas da wayoyin salula masu tsada daga hannunsu
Ofishin Hukumar yaki da cin hancin da rashawa (EFCC) na Ibadan ya kama wasu mutane 27 da ake zarginsu da yin danfara ta hanyar amfani da yanar gizo. An kamasu ne tare da wasu mata hudu da ake tunanin yan matansu ne.
KARANTA WANNAN: Trump da ya fadi dalilin sa na fasa kaiwa Iran hari
Mukaddashin mai magana da yawun hukumar, Tony Oriade, ya bayyana cewa jami’ansu sunyi kwantan bauna inda suka yi dirar mikiya suka kama yan danfarar. A cewarshi sun kama maza 27 da mata hudu da ake tunanin yan matan su ne
Ya ce “Jami’anmu sun fara bincike tsawon sati daya inda suka tattara bayanai game da barnar yan dan farar ‘yahoo-yahoo’ a wuraren da suke a fadin garin.”
“Bayanan da aka tattara bayanan na sirri ne, wanda hakan yayi sanadiyyar aikin da mukayi ranar Alhamis.’
“Cikin wadanda aka kama akwai; Adeleke peter, Babalola Abiodun,Adurajo Temitope, Abdulazeez Razak, Adesina Adewale, Osayintoba Dare, Adebowale fadairo, Abdulazeez Abdullahi, Akinseye Samuel da kuma Osanyintoba Femi.”
Ya kara da cewa hukumar ta kwato manyan motoci guda takwas ciki hadda katuwar motar Lexus guda biyu, da motoci kirar kamfanin Toyota guda shida da kuma manyan wayoyin salula masu tsada da kwamfitoci da dai sauransu.
Ya kara bayyana cewa “Wadanda aka kaman suna ikirarin sun kammala karatu wasu kuma na cikin yi a fannin karatun injiniyan kwamfita wasu kuma suka ce su yan kasuwa ne, a yanzu dai muna cigaba da bincike don sanin yawan laifuffukan da sukayi.”
“Za a kaisu kotu da zarar an gama bincike." A cewar Oriade.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng