An tsinci gawar wata budurwa 'yar shekaru 18 cikin jakar Ghana-must-go

An tsinci gawar wata budurwa 'yar shekaru 18 cikin jakar Ghana-must-go

An gano gawar wata budurwa mai shekaru 18, Favour Ogheneyenro a cikin jakar Ghana-must-go a garin Abraka da ke Ethiope Ta Gabas na Jihar Delta.

A cewar jaridar The Nation, an tsinci gawar ne a wani bola da ke bayan tashar Ozoro a garin Abraka.

Wadanda suka wurin da ake bude jakar sun ce akwai tabbai a wuyanta da ke nuna alamar makure ta akayi har sai da ta mutu.

Da ta ke kan yadda akayi 'yar uwarta ta bata, 'yar uwan marigayiyan, Maureen Sunday ta shaidawa 'Yan sanda ce wani na miji ya kira Favour a waya misalin karfe 10 na safe ya ce ta same shi a tashan Abraka.

Amma sai ta ce masa za ta tafi kasuwa tare da yayan ta.

DUBA WANNAN: Shuaibu ne ke yi wa Jam'iyyar PDP leken asiri - Shugabannin APC

Maureen ta cigaba da cewa a lokacin da suke hanyarsu ta zuwa kasuwar, wani matashi da ba ta taba gani ba ya tsayar da 'yar uwarta kuma suka yi magana kuma Favour ta hau babur ta bi shi.

Da aka tuntube shi, Kwamishinan 'Yan sanda na jihar Delta, Mr Adeyinka Adeleke ya ce kissar gilla ne.

Shugaban 'yan sandan kuma ya ce bayyana wanda ake zargi da kisar, ya ce saurain Favour ake zargi saboda ya tsere.

Da ya ke bayyani kan yadda aka kashe Favour, Adeleke ya ce: "Yarinyar da ake magana tana tare da 'yar uwarta lokacin da wani ya kira ta. Lokacin da za ta tafi ta fadawa 'yar uwarta cewa za ta tafi wurin saurayin ta ne.

"Daga lokacin ba sake ganin ta ba. Bayan kwana daya sai aka gano gawar ta a cikin buhu a gonar ayyaba.

"Saboda haka wannan ba matsafa bane kisar gilla ce. Alamun da ke wuyan ta sun nuna cewa an makure ta. Yanzu saurayin ta ya gudu.

"Idan bashi da hannu cikin abinda ya faru, mene yasa ya gudu? Mene ya sa ya tsere? Wannan shine abinda ya faru; ba matsafa bane kissar gilla ne. An kai gawar ta dakin ajiye gawarwaki."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel