Yan bindigan jihar Zamfara sun shimfida ka'idojin sulhu

Yan bindigan jihar Zamfara sun shimfida ka'idojin sulhu

Wasu sukace tashin hankali, barawo da sallama: Mun waye gari yan bindigan da suka addabi jihar Zamfara sun bada ka'idojin ajiye makamansu da kuma sulhu domin samun zaman lafiya a jihar.

Daya daga cikin ka'idojin da suka sanya shine a daina kashe yan Fulani musamman indo suka fita kasuwa.

Yan bindigan sun kara da cewa a bari su rika shiga kasuwanni ba tare da tsegumi ko tsoro ba.

Kwamishanan yan sandan jihar, Usman Nagoggo, ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yan banga da yan sakai. Nagoggo ya ce hukuma sun samu ganawa da yan bindigan kuma sunyi alkawarin cewa zasu daina kashe-kashe muddin an cika ka'idojinsu.

KU KARANTA: Jonathan ne ya bani Naira miliyan 400 ba Dasuki ba

Kwamishanan yace: "Daga cikin ka'idojin da suka sanya shine Yan sakai su daina kashe yan Fulani musamman a cikin kasuwanni."

"Yan bindigan sunce a rika bari suna shiga kasuwa ba tare da wani tsoro ko tsegumi ba."

"Wannan shine dalilin da ya sa muke wannan ganawar domin mu sanar da ku shirin zaman lafiyar da gwamnatin ta shirya."

"Yayinda yan banga suka kashe dan bindiga daya, su kuma suka kashe mutane 30, menene riban haka?"

Kwamishanan ya yi kira ga shugabannin yan sakai a jihar su yi bayani ga mabiyansu su daina kashe yan bindiga, saboda abinda ke kara hura wutar rikicin kenan.

A jawabin kungiyar yan sakai, sakataren kungiyar, Sani Babbar Doka, yace: "A sulhun da mukayi shekaru uku da suka wuce, mun ajiye makamanmu kamar yaddam gwamnati ta bukata amma yan bindigan basu ajiye ba."

"Shirye muke da yin duk abinda zai dawo da zaman lafiya al'ummarmu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel